Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya bayyana alhininsa kan yadda sojin saman Najeriya (NAF) suka musu barna sakamakon musayar wuta tsakaninsu da ‘yan bindiga.
Hakan ya faru ne sakamakon luguden wutar da NAF tayi wa ‘yan bindiga, wanda yayi sanadiyyar rasa rayukan wasu daga cikin mazauna karamar hukumar.
Gwamnan ya jajantawa iyalan wadanda suka samu raunuka tare da ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu tare da alkawarin bincike don gudun sake aukuwar lamarin.
Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mazauna yankin da suka rasa rayukansu yayin musayar wuta tsakanin sojin Najeriya da ‘yan bindiga a karamar hukumar Maru ta jihar.
Daily Trust ta rahoto cewa, Gwamnan ya bayyana alhininsa game da aukuwar lamarin a wata takarda da mai bashi shawara ta musamman a lamurran da suka shafi sadarwa, Zailani Bappa, ya fitar a ranar Talata.
Bappa ya ce gwamnan yayi takaicin jin labarin mara dadi yayin da sojin saman Najeriya suka yi fito na fito don sheke kungiyar ‘yan bindiga, amma cikin rashin sa a hakan ya ritsa da wasu mazauna yankin.
“Wannan lamarin mara dadi yazo ne a lokaci daya, yayin da sojin saman Najeriya suka fito gaba gadi don kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga, musamman ta hanyar yi musu luguden wuta.
“Zan so a madadin kaina da iyalina, da gwamnatin jiha da dukkan al’ummar jihar Zamfara in mika sakon jaje ga wadanda suka samu raunuka da mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon wannan barnar.”
– A cewar gwamnan, Ya kara da cewa, gwamnatin jihar tayi hobbasa don ganin ta shawo kan matsalar da hanzarta sanin musabbabin lamarin don gudun sake aukuwar lamarin a gaba.
A Wani labari na daban, dakarun sojin saman Najeriya sun kai samame kan ‘yan bindiga da suke addabar jama’a a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.
Wannan ya biyo bayan daukin gaggawa da jiragen yakin sojin suka kai bayan ‘yan bindiga sun tare babban titin Gusau zuwa Dansadau domin garkuwa da matafiya a kan babban titin.
Tuni sojin suka ragargaje su tare da aike wasu daga ciki barzahu.
Source:LegitHausa