Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ziyarci hedikwatar Hukumar Kula da Kera Motoci ta Kasa (NADDC) da ke Abuja, inda ya nemi hadin gwiwa da hadin gwiwa kan bai wa matasa jihar horo.
A yayin ziyarar, Gwamna Lawal ya samu tarba daga babban daraktan hukumar, Jelani Aliyu da manyan jami’an gudanarwarsa.
Gwamna Lawal ya bayyana shirin gwamnatin Jihar Zamfara na hada gwiwa da hukumar NADDC domin bai wa matasan jihar horo kan sana’o’in da ake bukata domin dogaro da kai.
“A yau, muna nan a matsayin wani bangare na kudiri na duba duk wata dama da za ta kara wa Jiharmu ta Zamfara daraja. Gwamnatina ta gano abubuwan da suka shafi tsaro, ilimi, noma da kuma ci gaban matasa.
“Na samu labarin cewa Hukumar NADDC ta gina Cibiyar Kera Motoci a Gusau, wadda har yanzu ba a fara aiki da ita ba. Gwamnatina za ta bada dukkan goyon bayan da ya dace don gudanar da ayyukanta cikin sauki. Muna kuma fatan samun karin hadin kai da zai inganta Zamfara.”
A nasa jawabin, babban daraktan hukumar ta NADDC, Jelani Aliyu, ya ce ziyarar da gwamna Lawal ya kai wani abin farin ciki ne da ke nuna irin jajircewar da sabuwar gwamnati ke da shi.
Ya kuma nuna jin dadinsa ga gwamnan bisa bai wa hukunar shawarar sanya ranar da cibiyar da ke Gusau za ta fara aiki.
Jelani ya bayyana cewa cibiyar ta kunshi kayan aiki don horarwa da gyara kayan aikin motoci.
Gwaman ta jadadda aniyarsa na bunkasa jihar ta hanyar bai wa mata tallafi da horo domin dogaro da kansu.