Shi ma Kabiru Ibrahim Masari abokin takarar tinubu ya tabbatar da cewa takardun shaidar duk karatun da ya yi sun bace.
Masari ya sanar da ‘yan sanda hakan, har ya rubuta takardar rantsuwa domin ya iya wanke kansa ‘Dan siyasar ya sanar da INEC cewa satifiket din duk makarantun da ya halarta sun bace a Abuja.
Kabiru Masari wanda zuwa yanzu shi Asiwaju Bola Tinubu ya bada a matsayin abokin takararsa a zaben 2023, ya ce takardun karatunsa sun bace.
Daily Trust ta rahoto cewa Alhaji Kabiru Masari ya fadawa hukumar zabe na kasa watau INEC cewa duk asalin takardun shaidar karatunsa, ba su hannunsa.
Kabiru Masari ya gabatarwa hukumar zabe na kasa da takardar rantsuwa ne a dalilin batar da takardun shaidar karatun firamare da sakandaren sa da ya yi.
‘Dan siyasar ya sanar da hukumar INEC cewa ya halarci makarantar firamare ta garin Masari daga 1972 zuwa 1978.
A yau shekaru 44 kenan da ya samu shaida.
An rahoto Masari yana cewa ya samu shaidar Grade 2 a makarantar Katsina Teachers College. Bayan nan kuma ya samu babban satifiket na malanta a 1995.
Babu wata shaida a kasa Zuwa yanzu ‘dan takaran mataimakin shugaban kasar na APC a 2023 bai iya bayyana wata shaida da za ta tabbatar da ya halarci wadannan makarantu ba.
Hakan ta sa abokin takarar na Tinubu ya yi rantsuwa a ofishin ‘yan sanda da ke unguwar Wuse 3 a Abuja, inda ya bayyana cewa takardunsa sun bace yana kan hanya a 2021.
Kamar yadda Masari ya shaidawa ‘yan sanda a rantsuwar da ya gabatar, ya ce takardunsa na asali sun bace da yake tafiya a yankin unguwar Wuse da ke Abuja.
An yi kokarin gano takardun, amma abin ya ci tura, kamar yadda Kabir Masari ya sanar da hukumar INEC yayin da ake tattara bayanin ‘yan takaran 2023.
Rantsuwar da Masari ya yi “Ni Ibrahim Kabiru Masari, namiji, Musulmi, ‘Dan Najeriya, mazaunin Abubakar Rimi Crescent, unguwar ‘yan majalisu, Apo, Abuja, na yi rantsuwa kamar haka: “Ni ne mai wannan suna da aka ambata, kuma asalin wanda ya mallaki wadannan takardu da aka ambata a kasa.”
“A Junairun 2021, a kan hanyar zuwa Wuse, na fahimci asalin takardar shaidar mallakar gida na NoKT 17522, GRA Katsina Estate, takardar shaidar Kaduna State Development Centre daga 1994-95; Shaidar Grade II daga Katsina Teachers College da shaidar First Leaving School daga makarantar First Leaving School Certificate daga 1979-83 sun bace.”
Takardun sauran ‘yan takara Ku na da labari cewa Hukumar INEC ta wallafa bayanai a game da masu neman takarar shugabancin kasar Najeriya a zaben da za ayi a farkon 2023.
Kowanensu ya gabatarwa Hukumar INEC mai zaman kan ta bayanin karatun da ya yi da aikinsa. A cikinsu Rabiu Kwankwaso ne yake da Difloma har zuwa PHD.