Jirgin rundunar sojin saman Najeriya ya tashi Bam a ƙauyen Mutumji, ƙaramar hukumar Maru, a jihar Zamfara.
Mazauna yankin sun bayyana cewa mafi yawan waɗanda suka mutu ‘yan ta’adda ne amma lamarin ya shafi fararen hula.
Bayanai sun nuna cewa akalla mutane 64 ne suka rasa rayukansu a samamen sojin bayan sun biyo ‘yan fashin jeji.
Aƙalla mutane 64 ne suka mutu a wani luguden wutan da Jirgin yakin Sojin Najeriya ya yi ranar Lahadi a ƙauyen Mutumji, ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara.
Mazauna yankin sun shaida wa jaridar Premium Times cewa mafi yawan mutanen da suka mutu ‘yan ta’adda ne, wasu kuma fararen hula ne mazauna garin.
Mutanen, da suka kunshi mata da ƙananan yara sun rasa rayuwarsu ne lokacin da Jirgin yakin ya tashi Bam a garin yayin da ya biyo ‘yan bindigan da suka gudo bayan sun kai hari.
A ranakun Asabar da Lahadi, rundunar Sojin saman Najeriya ta kai ɗauki kan kiran gaggawan da mutane suka yi bayan wasu yan bindiga sun kai faramki ƙauyukan Malele, Ruwan Tofa, da Yan-Awake a yankin.
Mazauna yankin sun tabbatar da cewa samamen sojin sama a kauyuka uku masu makwaftaka ya tilasta wa ‘yan ta’addan guduwa zuwa garin Mutumji mafi kusa don neman mafaka.
Wani mazauni, Nuhu Dansadau, yace ruwan wutan sojojin sama a kauyen Mutumji ya shafi fararen hula da dama, aƙalla mutane 64 suka mutu, wasu 12 suka jikkata.
Ɗansadau, mamban ƙungiyar kare hakkin ɗan adam, yace mutanen da duka ji rauni an tafi da su Asibitin Gusau, babban birnin jihar Zamfara domin duba lafiyarsu.
Haka zalika, magajin garin Mutumji, Abdulkadir Abdullahi, yace lamarin abun takaici ne da damuwa, har yanzun ana cigaba da kokarin tattara adadin mamatan.
Ku dakaci karin bayani…
Source:LegitHausa