Shugaban Hukumar NDLEA mai yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa Birgediya Buba Marwa (Ritaya) ya bayyana cewa akwai kimanin mutum miliyan biyu masu shan miyagun kwayoyi a jihar Kano. Marwa ya fadi hakan ne a yayin da ya ziyarci gwamnan jihar Kano a gidan Gwamnatin.
“A Jihar Kano, shan miyagun kwayoyi ya kai kimanin kaso 16 cikin 100; ma’ana a cikin duk mutum shida, daya dan kwaya ne, kuma alkaluman sun kunshi ’yan tsakanin shekara 15 zuwa 65 a duniya.” inji Buba Marwa
Sannan ya bayyana cewa karuwar ayyukan ta’addanci na da nasaba da karuwar aikata laifuka kamar su satar mutane, fashi da makami, ta’addanci da dai sauransu. Shugaban wanda kuma ya ce ya gamsu da rawar da Gwamnatin Jihar take takawa wajen yaki da dabi’ar, ya kuma ba da shawarar kafa dokar da za ta hana ’yan siyasa ba matasa miyagun kwayoyi. Kazalika, ya roki Gwamnatin da ta yi dokar da za ta tilasta wa masu son yin aure gwajin miyagun kwayoyin a matsayin wani matakin yaki da lamarin.