Ma’aikatar Lafiya a Faransa ta bayyana fargaba kan yiwuwar alkaluman masu kamuwa da sabon nau’in corona na Omicron ya kai mutum dubu 100 kowacce rana zuwa nan da karshen disamba, dai dai lokacin da kasashe ke tsaurara matakai don dakile yaduwar cutar a bangare guda China ta killace mutum miliyan 13 a yankin Xi’an.
Cikin kwanaki 7 da suka gabata dai Faransa na samun alkaluman mutum dubu 54 ne da ke harbuwa da cutar a kowacce rana sai dai minista Veran ya ce hasashen su na nuna yiwuwar alkaluman sukai dubu 100 kowacce rana a karshen disamba cikin yankunan kasar 35.
Karuwar alkaluman masu harbuwa da Omicron a sassan Duniya ya tilasta kasashe tsaurara matakai dakile yaduwar cutar, ciki har da China wadda ta killace ilahirin al’ummar yankin Xi’an fiye da miliyan 13.
Karkashin dokokin da China ta gindayawa yankin da ke arewacin kasar mutum daya cikin duk iyali guda ke da zarafin iya fita bayan kwanaki biyu don sayen abubuwa na wajibi.
Itama Sweden ta tsaurara matakan ko dai karbar rigakafi ko kuma gwajin da bai haura sa’o’I 48 ba kan matafiyan da ke shiga kasar yayinda Finland ta dauki makamancin matakin a yau laraba, a bangare guda kuma kasashen Portugal Ireland Cyprus da Latvia baya ga Italiya da Girka da Austria tuni suka gabatar da sabbin matakan kan masu shiga kasar baya takaita walwalar jama’arsu.