Mutum 17 sun mutu a hadarin mota kan hanyar Abuja.
Akalla mutum 17 ne aka ruwaito sun mutu, bayan wani mummunan hadarin mota da safiyar Talata a babban birnin Najeriya Abuja.
Lamarin ya faru ne a kan titin Kwali zuwa Abaji dake yankin na Abuja.
Hakama wasu mutum hudu sun jikkata, yayin da mutum daya bai samu ko kwarzane ba.
Kamar yadda mai magana da yawun hukumar kare hadurra ta kasar ya ce a wata sanarwa, hadarin ya hada da babbar motar Daf, da kuma bas samfurin Toyota, kuma gudun da ya wuce kima ne ya haifar da hadarin.
Bugu da kari sanarwar ta ce an gano akwai gajiya daga bangaren direban daya daga cikin motocin, lura da yadda suke shafe dare suna tuki ba tare da sun tsaya sun huta ba.
Tuni aka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa babbar asibitin Abaji, yayin da aka kai gawawwakin wadanda suka mutu zuwa dakin ajiye gawa na asibitin.
Read more :
Limamin Masallacin Quba da ke Madina ya rasu.
Martanin Sana’a game da satar man kasar Yamen: Ba mu kara yin gargadi ba; Mun bugi tankar.
Kauracewa ‘yan jaridan sahyoniyawan a gasar cin kofin duniya na Qatar.