Wani ganau ya bayyana cewa, hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da mutum 15, a yayin da suke kokarin haye kogin kauyen Lambara zuwa garin Shagari, inda hakan ya janyo wa mutuwarsu.
Duk da yawan kiran da ake yi wa gwamnatin Jihar Sakkwato na samar da jiragen ruwa na zamani da rigunan kariya ga matafiya a jirgin ruwa a jihar, amma babu abin da gwamnatin ta yi game da wannan kirayen-kirayen.
Sai dai, rundunar ‘yansandan jihar ba ta tabbatar da aukuwar lamarin da kuma adadin matafiyan da suka mutu ba a lokacin hada wannnan rahoto.
Wani mutum mazauni kauyen Illela Dabore da ke kusa da kauyen da hatsarin ya auku ya shaida wa Leadership cewa, mutune da dama sun rasa rayukansu tun bayan da tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya kafa Dam din a shekarar 2006.
A cewarsa, Dam din ya zamo wata annoba ga al’ummar yankin maimakon ya zamo abin alfahari a gare su, musamman idan aka yi la’akari da irin rayukan jama’a da suke rasa rayukansu a duk shekara saboda hatsarin jirgin ruwa, wanda hakan ya kasance hanya daya a gare su ta yin tafiye-tafiye.
Ya bayyana cewa, a yanzu haka, an iya gano gawarwakin maza 11 sai kuma ta mata guda hudu wadanda har yanzu ba a yi musu jana’iza ba kafin hada wannan rahoton.