Akalla mutum 14 ne Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) ta tabbatar da rasuwarsu a wani hatsarin mota da ya auku a kan babban hanyar Bauchi zuwa Darazo da ke Jihar Bauchi.
Hatsarin ya rutsa da mutum19 da suka hada da maza bakwai manya, mata manya 10, yarinya karama guda daya da karamin yaro daya sakamakon taho mu gama da motoci biyu suka yi da juna.
Kwamandan FRSC a Bauchi, Malam Abdullahi ne ya tabbatar da aukuwar hatsarin a ranar Alhamis, inda ya ce mutum biyar ne suka mutu.
A cewarsa, hatsarin ya hada da motoci guda biyu, wata motar kabu-kabu kirar Golf 3 Wagon mai lamba AJ507GWA da kuma mota kirar Chevrolet mai dauke da lamba 15B-07BA.
A cewar sanarwar, “Mutum biyar din da suka jikkata duka maza ne manya. Wadanda suka rasa rayukansu kuma su 14 ne, 10 manyan mata ne, biyu kuma manyan maza, sai wani karamin yaro guda da karamar yarinya daya.”
A cewar sanarwar, hatsarin ya faru ne sakamakon gudun wuce kima da direbobin motocin ke yi.
Daga cikin abubuwan da aka samo a wajen da hatsarin ya faru sun hada da kudi N73,000,00; wayoyin salula guda bakwai da sauransu kayayyaki.
Jami’an FRSC sun kai dauki wajen da hatsarin ya faru, inda suka kwashi gawarwakin da suka mutu da wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH), Bauchi, yayin da likita ya tabbatar da adadin da suka mutu da kuma kula da lafiyar wadanda suka jikkata.
Source:LeadershipHausa