Mutane fiye da 60 sun bata bayan ambaliyar ruwa a Afirca ta Kudu .
Ana ci gaba da neman mutane 63 da suka bata bayan ambaliyar ruwan da aka yi a yankin KwaZulu-Natal na kasar Afirca ta Kudu a makon jiya.
Mutane fiye da 440 ne suka mutu sanadin ambaliyar ruwan, ciki har da ma’aikatan agajin gaggawa biyu.
Mamakon ruwan sama da ya cika koguna yankin da zaftarewar kasa ne suka yi awon-gaba da mutanen.
Gwamnati ta ayyana KwaZulu-Natal a matsayin yankin da ke fama da bala’i bayan jami’a sun bayyana cewa ambaliyar ruwan na cikin mafi muni da ta faru a yankin a tsawon tarihi.
READ MORE : Iraqi Ta Kira Jakadanta A Sweden Bayan Kona Al Kur’ani A Kasar.
Firimiyan KwaZulu-Natal Sihle Zikalala ya ce ambaliyar ruwan ta rusa kusan gidaje 4,000 sannan ta lalata gidaje fiye da 8,000, galibi a birnin Durban da ke kusa da tashar jiragen ruwa da ma garuruwan da ke kusa da shi.