Har zuwa yanzu da muke hada wannan rahoton babu wanda yasan ina wadannan mutane suke, wadanda a watan augustan wannan shekara ta 2021 mataimakin shugaban majalisar wakilan najeriya Hon Ahmad Wase, ya tabbatar da cewa an kaisu kasar isra’ila an basu horon aiwatar da ayyukan ta’addanci kuma sun dawo gida najeriya.
Tun watan augustan wannan shekarar dan majalisar mai wakiltar mazabar wase yace wasu daga cikin ‘yan siyasar najeriya sun kai mutane 300 isra’ila kuma anyi wa wadannan mutane horo na musamman domin aiwatar da ayyukan ta’addanci a najeriya amma abin takaici har yanzu babu wanda ya san ina wadanann mutane suke kuma an da tabbacin sun dawo najeriya.
Babban dalilin da zai tabbatar da cewa sun sun dawo najeriya shine, yadda ake ta samun tashe tashen hankula a na da can wanda duk hakan yana nyna tasirin ayyukan wadannan horarraun ta’addancin kasar isra’ilan ne.
Honarable wase ya tabbatarwa da majalisa cewa, yana sane sarai cewa rayuwar sa tana cikin hadari amma dai dole ya fadi gaskiya domin ya lura abubuwa suna nema su zama sun fi karfin hukumomi musamman a mazabar sa wacce yace a can wadannan wadannan ‘yan ta’addan da aka yima horo a isra’ila sukafi tasiri.
Abin mamaki dangane da bayanin da honorable wase yayi shine, har zuwa yanzu babu wanda ya musa ko ya karyata kuma bamu samu labarin gwamnatin najeriya ta kira jakadan isra’ila a najeriya domin bin bahasin wannan mummunan al’amari wanda yake cin rayukan ‘yan najeriya akullum rana, babu ji babu gani.
Shin da gaske gwamnatin najeriya take wajen kawo karshen tashe tashen hankula kuwa? indai ba haka ba yaya dan majalisa mai daraja zai bada bayanin tsaro kuma mai mihmmanci irin wannan kumayi burus da lamarin.
Ita dai haramtacciyar kasar isra’ila kowa ya san ta shahara da ta’addanci da kuma daurewa ta’addanci gindi, ko ba komi me kake tsammani daga yahudawan sahayoniya?