Hatsarin mota ya yi sanadin rasuwar mutane uku da jikkata wasu da dama a karamar hukumar Takai na Jihar Kano.
Hatsarin ya faru ne tsakanin wata bus mai dauke da mutum 15 da Toyota Hilux mai dauke da mutum uku.
Saminu Yusuf, kakakin hukumar kwana-kwana ta Jihar Kano ya tabbatar da afkuwar hatsarin ya kuma bayyana sunayen wadanda suka rasu.
Mutane uku sun rasu, yayin da wasu 15 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya faru a karamar hukumar Takai ta Jihar Kano, Daily Trust ta rahoto.
Hukumar kwana-kwana ta Jihar Kano ta tabbatar da afkuwar lamarin ta bakin kakakinta, Mista Saminu Yusuf, a ranar Lahadi.
Ya ce hatsarin ya ritsa da wata Toyota Hilux ne da ke dauke da mutum 3 daga Jigawa da wata motar bas ta haya mai dauke da mutum 15 daga Kano.
A cewarsa, bayan motoccin sun yi karo, bas din ta kama da wuta kuma aka ceto mutum uku a sume, yayin da sauran suka jikkata.
Ya ce: “Bayan samun bayanin, mun tura tawagarmu ta bada dauki cikin gaggawa.
“Da isarsu, sun gano cewa motar bas ta haya (hummer) mara lamba dauke da mutum 15 ce ta yi karo da Toyota Hilux mai dauke da mutum uku daga Jigawa mai lamba JMK 142 XA.
Bas din ta kama da wuta. “Cikin mutum 18 da hatsarin ya ritsa da su, an ceto mutum 15 da ransu yayin da an ceto uku cikin fasinjojin bas din a sume.
Nan take muka kai su Babban Asibitin Takai inda likitoci suka tabbatar mutum ukun da aka ceto a sume sun mutu.”
Abdullahi ya ce wadanda suka rasun sune Sani Isah, mai shekara 28; Shamawilu Isah, mai shekara 30 da Yusuf Musa, mai shekara 32.
Ya shawarci masu motocci su rika taka-tsantsan yayin tuki.
A wani rahoton, kwamishinan Matasa Da Wasanni na Jihar Yobe, Hon. Goni Bukar Lawan, (BUGON) ya mutu a hatsarin mota kan hanyar Damaturu zuwa Kano.
Goni Bukar, tsohon dan majalisar wakilai na tarayya, wanda aka fi sani da BUGOM, ya rasu a daren yau Talata a hanyarsa na zuwa Jihar Kano, Leadership ta rahoto.