Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin zamani, Farfesa Isa Pantami, ya bayyana cewa bangaren sadarwa muna fifita tsaro akan amfanin tattalin arziki.
A cewarsa, Ma’aikatar ba ta wasa da tsaro, yana mai cewa tana taimaka wa cibiyoyin tsaro kuma hakan yana haifar da illa ga cigaban tattalin arzikin ma’aikatar sadarwa.
“Har ma muna yin illa ga ci gaban tattalin arzikin sashin mu saboda manufar mu ta tallafawa cibiyoyin tsaro.
“A kowane lokaci a cikin sashin sadarwa matsayin mu shine ‘tsaro shine fifiko akan amfanin tattalin arziki’.
“Tsaro shine fifikon mu bayan amfanin tattalin arziki. Amma idan abubuwa biyu za a iya bi, wannan shine fifikon mu.
amma sai dai alamu suna nuna kalaman ministan basu da wata ma’ana domin ta kai yanzu a kan iya waya ta kwanaki da masu garkuwa da mutane kuma basui canja layi ba amma hukumomi basa iya bibiyar layin ‘yan ta’addan domin dakile ayyukan su na ta’addanci.
A gaskiya dai ana ganin wadannan zasu iya zamna kalaman romon baka daga bakin ministan amma dai a gaskiyar lamari ma’aikatar sa bata da wata shaida da zata tabbatarwa da al’ummar najeriya cewa tana aiki ka’in da na’in domin dakile ayyukan ta’addanci da ake cigaba da aiwatarwa a fadin kasar.
Ayyukan ta’addanci dai sai cigaba suke a fadin najeriya kuma gwamnati ta kasa takawa lamarin birki yayin ta talakawa ke ta kukan cewa ”muna cikin tashin hakalin da bukatar taimako daga gwamnati” amma gwamnati taki daukan mataki illah zantukan romon baka marasa tushe irin na minsta fantami.