Mai magana da yawun kungiyar ma su safarar jakuna da dawaki a Nijeriya “National Association of Donkeys Marchants” (NADM), ya bayyana cewa mun dauki matakin kafa hadaddiyar kungiyar ne don inganta harkokin kasuwancinsu tare da sha alwashin fuskantar kalubalen mambobin kungiyar ke fuskanta a kasar nan, da shailanta bayar da tasu gudumawa wajen hadin kan yan kasa, bunkasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi ga matasa.
Gamayyar yan kasuwar sun bayyana hakan a tattaunawar da wakilinmu ya yi jami’in hulda da jama’a a kwamitin rikon kungiyar na kasa, Alhaji Mai Saleh Tijjani Gaidam, jim kadan da kammala babban taron da suka gudanar a Gashuwa ta jihar Yobe, wanda ya gudana karshen mako wanda suka zabi shugabanin rikon kwarya don gudanar da al’amurran kungiyar da share fagen da zai kai ga zaben shugabaninta na din-din-din a kasa baki daya. Haka kuma ta bayyana cewa sun kafa kungiyar ne domin magance matsalolin da harkokin kasuwancin dabbobin ke fuskanta da kokarin kawo gyara ta hanyar daukar ingantattun matakai wajen biyayya ga dokokin kasa da manufofi masu ma’ana kan farfado da tattalin arzikin Nijeriya.
Bugu da kari, taron ya samu halartar mambobin kungiyar daga sassan kasar nan, haka kuma an zabi shugabanin kwamitin rikon kwaryar da zai tafiyar da harkokin kungiyar wanda suka kunshi Alhaji Salisu Yunusa a matsayin shugaban rikon kwarya na kasa, sai Mista Cheif Godwin Ishiali a matsayin sakatare, yayin da Alhaji Abdullahi Adamu zai rike ma’ajin kwamitin kana kuma shugaba a jihar Yobe, Mai Saleh Tijjani a matsayin jami’in hulda da jama’a. A hannu guda kuma, taron ya yi armashi saboda yadda ya gudana cikin tsanaki da samun amincewar kowane bangare.
Haka zalika kuma, Mai Saleh ya kara da cewa ganin irin yadda wannan kasuwanci ya dade kuma wanda yake gudana a kowane lungu da sakon kasar nan tsawon shekaru masu yawan gaske, kuma kasuwanci ne da su ka gada kaka da kakani, sannan mai tarihi da tasiri a al’ada, musamman a arewacin Nijeriya da bayar da gagarumar gudumawa a sha’anin zirga-zirgar jama’a da kaya a zamanna masu tsawo da yanzu, ta hanyar amfani da jakuna da dawaki hadi da sauran dabbobi zuwa kusan kowane bangaren kasar nan, wanda yanzu lokaci ya yi wanda za a bunkasa shi don cin gajiyarsa. Ya ce duk da yadda ake samun canje-canje dangane da yadda kasuwanci ke gudana wanda ya na daga cikin dalilan da suka sanya mun fara tunanin kafa kungiyar wadda za su yi mata rijista don hada kan yan kasuwar tare da ingantata.
Babban jami’in hulda da jama’ar ya shaidar da cewa, “Abu na farko shi ne, baya ga yadda wannan kasuwancin ke taimaka wa wajen samar wa da matasa da sauran jama’a hanyar cin abinci da sa mun hanyar dogaro da kai wajen neman na kansu, haka kuma yan kasuwar mu su na taimaka wa sosai wajen samar da ayyukan yi da rage zaman kashe wando. Sannan kuma ya na samar wa gwamnatin Nijeriya kudin shiga, wanda ya kunshi haraji da kudin shiga na kimanin miliyoyin naira a kowace shekara, wanda ta la’akari da alfanun da yake dashi muka yanke shawarar kafa hadaddiyar kungiya ta kasa, wanda ko shakka babu za ta taimaka wa gwamnati ta fuskoki da dama a daidai wannan lokaci wanda tattalin arzikin duniya ke fama da kalubale ta dalilin annobar korona da sauran tarnaki.”
“Saboda haka idan ka duba wannan ba karamar gudumawa ya ke bai wa gwamnatocin kananan hukumomi, jihohi da tarayya ba. Domin kasuwanin karkara mun dinga sayo dabbobin nan, mu biya haraji a matakai daban-daban, a saka a mota ko mu biya mutane su kora zuwa inda tashoshin da muke loda wa a manyan motocin dakon kaya zuwa kowane bangare a kasar nan. Wanda gwamnati da al’umma ke cin gajiyar kasuwancin kusan kowace rana. Al’amarin da ke taimaka wa bunkasar tattalin arzikin al’umma tare da kasar mu baki daya.” Ta bakin Alhaji Tijjani.
“Har wala yau, mu na yan kasuwar da sun zarta mutum 10,000 wadanda ke gudanar da kasuwancin jakuna da dawaki, daga kowane bangaren kasar nan, wadanda kuma suke samar wa dubban matasa ayyukan yi, kuma ta wannan dalili muka yanke shawarar kafa kungiya ta kasa wadda za ta samu wakilcin kowane bangare a Nijeriya, sannan kuma shalkwatar kungiyar mu tana jihar Ebony tare da rassa a jihohi da dama a fadin kasar nan.”
Ya kara da cewa, sakamakon tuntuba da shawarwari daga bakin kwararru da masana ya jawo su ka yi tunanin kafa kungiyar wadda za ta yi magana da yawun yayanta, sannan ya kara da cewa a halin da ake ciki su na fadi tashin yi wa kungiyar rijista ta kasa wanda zai ba ta cikakkiyar dama da ikon gudanar da ayyukan ta karkashin dokoki da tsare-tsaren da kundin tsarin mulkin Nijeriya suka shata kamar kowace kungiya a kasar nan, ya ce hakan zai taimaka wajen sanya ido da daukar matakai wajen mambobin suna biyayya ga dokokin Nijeriya a matsayin yan kasa nagari masu kokarin ganin ta ci gaba ta kowace fuska.
“Dangane da wannan, mun bai wa gwamnatin tarayya tabbacin samun hadin kan yayan kungiyar NADM tare da cikakken goyon baya dangane da manufofi da kudurorin da ta sanya a gaba domin samun hadin kan yan kasa da bunkasar tattalin arziki. Haka kuma muna kira ga daukwacin mambobinmu a fadin kasar nan, su kasance masu da’a da biyayya ga dokokin kasa tare da aiki tukuru wajen ci gaban kasarmu Nijeriya. Haka kuma, muna kira da babbar murya ga dukanin yayan kungiyar su bai wa shugabaninta cikakken goyon baya wajen samun nasarorin da aka sanya a gaba, wanda ta haka ne zai taimaka wajen ginata kuma ta bunkasa don ci gaba.” Ta bakinsa.