Cikin muhamman batutuwan wanna sati a kwai cewa , ‘Dan takarar kujerar shugabancin kasa a karkashin APC, Bola Tinubu ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a matsayin abokin tafiyar sa.
Bayan Tinubu ya yi wannan sanarwar, ‘yan Najeriya zasu so sanin karin bayani game da wannan ‘dan siyasan haifaffan jihar Borno Shettima makusancin Tinubu kuma ‘dan gani-kasheninsa, mai masa yakin neman zabe tun kafin ya ci zaben fidda gwani na jam’iyyar APC.
A ranar Lahadi 10 ga watan Yulin 2022 ne ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da Sanata Kashim Shettima na Borno a matsayin abokin tafiyarsa a zaben 2023 mai zuwa.
Tinubu ya tabbatar da zabin Shettima a yayin zantawa da manema labarai a garin su shugaban kasa Muhammadu Buhari, Daura dake jihar Katsina.
‘Dan takarar jam’iyyar APC ya je har garin Daura ne domin mika gaisuwar sallah babba da aka yi a ranar Asabar ga shugaban kasa.
Legit.ng ta zakulo muku tare da nemo muku muhimman abubuwan da ya dace ku sani game da ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC a zaben 2023.
An haifi Shettima a Maiduguri dake jihar Borno a ranar 2 ga watan Satumban 1966 a gidan Sir Kashim Ibrahim.
A halin yanzu yana da shekaru 55 a duniya kuma kabilar Kanuri ne.
Tsohon gwamnan jihar Borno ne wanda ya mulka jihar tsakanin 2007 zuwa 2015 kuma Sanata ne mai ci a yanzu wanda aka zaba tun 2015 domin ya wakilci mazabar Borno ta tsakiya a majalisar dattawa.
Yana da digirinsa na farko daga jami’ar Maiduguri inda ya karanci tattalin arziki na harkar noma da kiwo kuma yayi digirin digo a wannan fannin daga jami’ar Ibadan.
Ya yi hidimar kasarsa a tsohon bankin manoma na Najeriya dake Kalaba, babban birnin jihar Cross River daga 1989 zuwa 1990.
Shettima ya koma jami’ar Maiduguri a matsayin malami mai koyarwa a sashin tattalin arziki na noma da kiwo kuma ya kwashe shekaru 2 yana aikin.
Shettima kwarraren ma’aikacin banki ne kuma masani a fannin tattalin arziki kafin ya fada siyasa. Daga 2007 zuwa 2011, ya rike kwamishina a ma’aikatu biyar.
Yana auren Nana Shettima kuma sun haifa yara uku, Mata biyu da yaro namiji daya.