‘Yan bindiga a Birnin Gwani ta jihar Kaduna sun sako wasu mutane 12 bayan karbar mudu 20 na shinkafa, 20 na wake, jarkar manja, man gyada da katin waya na N10,000 a matsayin fansa.
Amma an ruwaito cewa, ‘yan bindigan sun hallaka wani manoma tare da yin awon gaba da mutane 20 daga gonakinsu a yankin Jangali da Kwaga duk dai a yankin Birnin Gwani.
Kungiyar ci gaban masarautar Birnin (BERU) ce ta fitar da sanarwar hakan ta hannun shugabanta, Ishaq Usman Kasai a jiya Alhamis 29 ga watan Satumba.
Ya kuma bayyana cewa, ‘yan bindigan sun nemi Naira miliyan 12 a matsyain kudin fansa daga wasu manoman da suka sace. A cewar sanarwar: DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka.
“An sako mutum hudu da aka sace a Unguwar Liman da kuma daya da aka sace a unguwar shekarau a jiya Laraba bayan biyan miliyan 2 da N500,000 bi da bi.”
“Manoma biyar da aka sace a ranar Alhamis 15/9/2022 a Kurgin Gabas da Sabin Layi sun yi nasarar kubuta daga maboyar ‘yan bindiga bayan shafe mako guda a can. ”
Abin bakin ciki, an kashe wani manomi a yankin Shiwaka ranan Talata 27/9/2022 bayan daure shi a jikin bishiya; kuma sama da mutum 20 aka sace a ranar Laraba 28/9/2022.”
Source:legithausang