Ƙasar Morocco ta kafa tarihin zama ƙasa ta farko daga nahiyar Afirka da ta kai wasan kusa da na ƙarshe (Semi Final) a gasar cin Kofin Duniya a Tarihi.
Channels tv ta tattaro cewa tawagar ‘yan wasan Morocco sun kai ga nasara ne bayan Youssef En-Nesyri ya jefa kwallo a raga kafin zuwa hutun rabin lokaci a wasan da suka lallasa Portugal da ci ɗaya mai ban haushi.
Atlas Lions kamar yadda ake wa ‘yan wasan laƙabi sun sake kafa tarihin zama Larabawa na farko da suka kai zagayen zakaru huɗu a wasan da ya gudana ranar Asabar a filin Al-Thumama, Qatar.
Ana ganin mai yuwuwa fitaccen ɗan wasan nan, Cristiano Ronaldo, ya buga wasansa na ƙarshe a gasar Kofin duniya bayan an sako shi a matsayin canji.
Sai dai duk da sako zaƙaƙurin ɗan wasan ya gaza jefa kwalllo a raga ta farko tun bayna fara wasannin kifa ɗaya kwala a gasar.
Ku saurati ƙarin bayani.
A wani labarin na daban kimanin mako guda daga dawowa daga kasar Guinea, Shugaban kasa zai sake tafiyar kasar waje.
Shugaban kasar Amurka ne ya gayyacesa, a cewar masu magana da yawin shugaban kasan.
Kusan kowace shekara sai shugaba Buhari ya ziyarci Amurka halartan taron majalisar dinkin duniya.
Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Lahadi, 11 ga watan Disamba zai tafi birnin Washington, kasar Amurka domin halartan taron hadakar nahiyar Afrika da Amurka.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar ranar Asabar, rahoton DailyTrust.
Ya bayyana cewa za’ayi taron ne tsakanin ranar Talata, 13 ga Disamba zuwa 15 ga Disamba, 2022.
A cewarsa, shugaban kasa Amurka, Joe Biden, ne ya gayyaci shugabannin kasashen Afrika.
Ya ce wannan taron za’a yisa ne domin karfafa alakar nahiyar Afrika da Amurka wajen zuba hannun jari da sauransu.
Shugaba Buhari zai samu rakiyar wasu gwamnoni, ministoci, shugabanin hukumomin tsaro, da wasu manyan jami’an tsaro.
Gwamnonin sun hada da Gwamna Bala AbdulKadir Mohammed na jihar Bauchi da kuma AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara.
A karshe, ya ce shugaban zai dawo ranar Lahadi, 18 ga Disamba, 2022.