Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP, Mista Peter Obi ya ce, idan ‘yan Nijeriya suka zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben 2023, gwamnatinsa za ta goyi bayan duk wani shiri da zai kara bunkasa fannin tattalin arzikin Nijeriya.
Mista Obi, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da Diran Onifade, shugaban sashen yada labarai na yakin neman zaben Obi-Datti, ya aikawa jaridar LEADERSHIP a daren jiya lahadi.
Sanarwar ta ce, peter Obi ya bayyana hakan ne a martanin da ya mayar akan wani rahoton da aka wallafa na cewa, baya goyon bayan shirin fara hako man fetur a jihohin Bauchi da Gombe da ke a yankin na Arewa maso gabas.
A cewar sanarwar, bayan kudirin da dan takarar ya fitar a taron gangamin yakin nemansa a garin Ibadan cikin jihar Oyo, wanda kuma kafafen yada labarai suka wallfa, babu wata hira da ya yi da wani dan jarida a bayan fagen gangamin.
Ya ce, rahoton karya ce tsagwaron ta, an kuma wallafa hakan ne don a bata masa suna da bata tafiyar sa ta neman shugabancin kasar nan.
Bayan gano man fetur a arewacin Najeriya dai wasu na adawa da fara hako man fetur din a arewan saboda wasu manufofin su kan yankin.
Source:Leadership