Gabon – Ministan harkokin kasashen waje na kasar Gabon, Michael Moussa Adamo, ya rasu ranar Jumu’a sakamakon bugawar zuciya yayin da yake jiran shiga taron majalisar zartaswa.
A wata gajeruwar sanarwa da gwamnatin Gabon ta fitar ta bayyana cewa Moussa Adamo, ɗan shekara 62 ya rasu bayan fama da bugun zuciya duk da kokarin kwararrun Likitoci na ceto shi.
“Ya zauna a ɗakin jira mintuna kaɗan gabanin fara taron majalisar ministoci, a gaban wasu daga cikin abokan aikinsa a gwamnati ya fara jin alamun rashin lafiya.”
Wata majiya da ta nemi a sakaya bayananta tace an yi hanzarin kai Ministan Asbitin Sojoji yayin da abun ya tsananta amma rai ya yi halinsu da tsakar rana.
Wannan babban rashi ne ga ƙasar Gabon
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa da yake martani kan lamarin, shugaban ƙasa Bango ya ayyana marigayi Moussa Adamo a matsayin abokin hulda kuma dattijon ƙasa.
“Tun fari ya kasance aboki, mai biyayya da yakini, wanda a ko da yaushe nake lissafa shi a sahun farko.
Wannan ba karamin rashi bane ga kasar Gabon,” inji shugaban kasa.
An haifi Moussa Adamo a garin Makokou dake arewa maso gabashin Gabon a shekarar 1961 kuma ya far aiki ne a matsayin mai gabatarsa a gidan Talabijin.
A 2000, ana naɗa shi shugaban ma’aikata ga Ministan tsaro, wanda a wancan lokacin shi ne Bango, shugaban kasa mai ci a yanzu.
Lokacin da aka zabi Bango a matsayin shugaban kasa bayan rasuwar mahaifinsa Omar Bongo Ondimba, a 2009, Moussa Adamo ya koma matsayin mashawarci na musamman.
Bayan shekaru 10 a matsayin Ambasadan Gabon a kasar Amurka zuwa 2020, ya zama Ministan tsaro daga baya kuma ya koma Ministan harkokin waje a watan Maris na bara. Ku saurari karin bayani…
Source:LegitHausang