Karamin ministan Buhari, Festus Keyamo (SAN) ya yabi zabin Sanatan Borno, Kashim Shettima da Bola Ahmed Tinubu ya yi.
Karamin Ministan kwadago da samar da ayyukan yi yana ganin Kashim Shettima ya fi kowa cancanta Keyamo yake cewa Sanata Shettima yana da biyayya, ya san kan aiki, kuma matashi ne shi Abuja.
Karamin Ministan kwadago da samar da ayyukan yi na kasa, Festus Keyamo (SAN), yana cikin wadanda suka yabi zabin Kashim Shettima.
Festus Keyamo (SAN) ya yi magana a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 9 ga watan Yuli 2022, yana mai cewa Kashim Shettima ya dace da takara.
Sanata Kashim Shettima shi ne wanda ‘dan takaran kujeran shugaban kas ana APC watau Bola Ahmed Tinubu ya dauko a matsayin abokin takara.
Tun ranar aka ji karamin Ministan yana jero dalilan da suka sa tsohon gwamnan na jihar Borno ya dace da ya zama mataimakin shugaban Najeriya.
Sanatan na Borno ta tsakiya na kin-karawa, yake cewa sam bai da hayaniya, duk da karancin shekarunsa (59), ya san kan aiki sosai.
Bugu da kari, Kashim Shettima ya lakanci ilmin tattalin arziki da tsimi, wanda aka san mataimakin shugaban kasa yana taka rawa a wannan fanni.
Keyamo yana ganin bai dace a tsaya duba addini yayin da ake neman cigaba ba. The Cable ta rahoto Lauyan yana cewa Babarbaren ya fi kowa cancanta da wannan matsayi.
“Kwararren ma’aikacin banki, mai ilmin tattalin arziki, mara hayaniya – mutum kuma ‘dan siyasa mai kan-kan da kai. “Mai kaifin basira, masanin tattalin arziki, matashi kuma wanda ya san kan aiki, tsani tsakanin zamanin yau da na baya.”
“Mai matukar biyayya, zai taimakawa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Shettima ya fi kowa dace da kujerar mataimaki.”
Festus Keyamo Tinubu ya tada kura Ku na da labari Asiwaju Bola Tinubu wanda Musulmi ne ya tsaida Kashim Shettima, wani Musulmin daga Arewa maso gabas a matsayin Abokin takararsa. Barista Daniel H. Bwala wanda ya taba zama Mai ba APC shawara a kan sha’anin shari’a ya fice daga jam’iyyar saboda an hana Kirista tikiti a zaben 2023.