Ministan Buhari, Bashir Magashi ya ce gwamnatin tarayya za ta tabbatar da ganin cewa hukumomin tsaro sun fara samun jawabin gargadi daga kasashen waje kafin su isa ga jama’a.
Ministan tsaron ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 1 ga watan Nuwamba, yayin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai.
An dai shiga halin fargaba a kasar a baya-bayan nan sakamakon gargadin da kasashen US da UK suka yin a yuwuwar kai hari a Abuja.
Ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya, ya ce addu’a Najeriya ke bukata daga gwamnatin Amurka maimakon gargaji wanda ya jefa mutane cikin rudani.
Ministan ya bayyana cewa gargadin da Amurka tayi kan yuwuwar kai harin ta’addanci a Abuja ya jefa jama’a cikin tsoro sannan ya razanar da yan Najeriya ta yadda har sun gaza daukar matakin da ya dace, rahoton Vanguard.
Sai dai kuma, ya bayyana cewa barazanar bai yi tsanani ba, yana mai bayar da tabbacin cewa gwamnati na kan lamarin da taimakon hukumomin tsaro da na leken asiri.
Magashi ya yi magana ne yayin da yake kare kasafin kudin ma’aikatar tsaro na 2023 a gaban kwamitin majalisar wakilai, rahoton The Cable.
Jawabin sa martani ne kai tsaye ga wata tambaya da shugaban kwamitin majalisar, Hon. Babajimi Banson yayi kan abun da yake yi don magance gargadin da wasu kasashen waje ciki harda Amurka suka yi kan tsaro.
Magashi ya ce: “Idan kun tuna, a jiya kwamitin tsaro sun gana sannan mun tattauna wannan barazanar kuma mun yarda cewa ba abu ne da zamu yiwa rikon sakainar kashi ba.
Mun yi kokarin tabbatar fa tushen barazanar ko jawabin da gwamnatin Amurka tayi.
Mun yi kokarin gano kasashen da ke da ra’ayi a jawabin da gwamnatin Amurka tayi kuma mun ga cewa hanya mafi dacewa da za a bi da lamarin shine ci gaba da tsaurara matakan tsaro a Abuja da jihohin da ke makwabtaka, wato Nasarawa, Neja da sauransu.
“Sai dai kuma, mun yarda cewa ruwa baya tsami banza kuma dangane da hakan, mun yi nasarar gabatar da lamarin ga hukumomin leken asirinmu kuma sun gabatar da amsoshi a wuraren da gwamnati ke shakku kuma mun gano cewa muna bukatar sanya idanu sosai don hana duk wasu ayyukan yan bindiga, wanda daga nan ne barazanar zai iya faruwa, za mu samar da isassun runduna da za su iya kawar da irin wadannan lamuran.
“Ina mai ba mambobin majalisa tabbacin cewa gwamnati na kan lamarin.
Bisa ga taron tsaro da abun da muke da su a kasa, ina ganin abun da muke bukata daga Amurka addu’a ce ba wai bamu bayanan da zai jefa al’ummarmu a rudani ko rashin daukar matakin da ya dace.
Kuma ministanmu na harkokin waje zai dauki mataki kan wannan don ganin cewa an gabatar bayani irin haka a gaban ma’aikatar kafin watsa shi cikin al’umma.
“Ina ganin muna kan lamarin. Barazanar bai yi tsanani ba kuma muna daukar mataki.
Muna yin duk wanda zamu iya don tabbatar da ci gaba da zaman lafiya a Najeriya.
Source:leguthausang