Miliyoyin ƴan Najeriya na zaɓen sabon shugaban ƙasa
Miliyoyin ‘yan Najeriya na kaɗa ƙuri’a a zaben da kusan dukkan ‘yan takarar suka kawo jiki, a karon farko tun da mulkin soja ya kau daga ƙasar.
Tun 1999, jam’iyyun siyasa biyu ne suka mamaye fagen siyasar ƙasar – jam’iyyar APC mai mulki da ta PDP.
Amma a wannan karon, akwai wasu ‘yan takara biyu da suka kawo jiki – Peter Obi na jam’iyyar Labour da Rabiu Musa Kwankwaso.
Shugaba mai-ci Muhammadu Buhari zai sauka daga muƙaminsa bayan ya kammala wa’adi biyu masu tsawon shekara takwas.
Jam’iyyarsa ta All Progressives Congress (APC) ta naɗa tsohon gwamnan jihar Legas Ahmed Bola Tinubu ya jaorance ta a wannan zaben, inda shi kuma tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ke jagorantar babbar jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP).
Akwai jimillar ‘yan takara 18 da suka tsaya takarara mukamin shugaban ƙasa.
Gabanin wannan zaben, ‘yan Najeriya sun fuskanci ƙarancin takardun kuɗin ƙasar wato Naira a dalilin wani shirin sauya fasalin takardun kuɗin da ya gamu da matsananciyar tangarɗa.
Lamarin da ya haifar da ruɗani a bankunan da ke faɗin ƙasar har ma a wuraren da ake hada-hadar kuɗaɗe yayin da ‘yan ƙasar ke matukar buƙatar kuɗaɗensu.
Gwamnatin ƙasar ta samar da sababbin takardun kuɗin ne domin ta magance hauhawar farashin kayayyaki da kuma magance amfani da kuɗi domin sayen ƙuri’u.
Ana jajibirin wannan zaɓen, jami’an tsaro suka kama wani dan majalisar wakilai yayin da yake ɗauke da kusan dala 500,000 na garin kuɗi har ma an gano wani jadawalin sunayen waɗanda ya so ya rabawa kuɗin, kamar yadda ‘yan sanda suka sanar.
Tilas ne ga ɗan takarar da ya lashe wannan zaben ya mayar da hankalinsa kan wannan batun na sauyin fasalin takardun naira, da kuma matsalar tattalin arziƙi mai ƙara tabarbarewa da rashin aikin yi musamman tsakanin matasa da kuma rashin tsaro da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 10,000 a bara kawai.
Bayan da wasu ‘yan bindiga daga ƙungiyar IPOB suka kashe wani dan takarar mukamin majalisar dattawa a ranar Laraba, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ɗage zaɓe a mazaɓar da ya fito a jihar Enugu da ke yankin kudu maso gabashin Najeriya.
Wannan zaben ya ja hankulan matasa da waɗanda wannan ne karonsu na farko da za su yi zabe – waɗanda ke da kashi daya cikin uku na masu kaɗa ƙuri’a miliyan 87 da suka cancanci su kaɗa ƙuri’a – lamarin da ka iya sa ɗumbin masu zaɓe su halarci runfunan zaɓen har su iya zarce kashi 35 cikin 100 na jimillar alƙaluman waɗanda suka yi zaɓe a 2019.
“Wannan ya kasance aikina kuma na ga muhimmancin yin zaɓe,” inji Blessing Ememumodak, wata mai shekara 19 da haihuwa yayin wata ganawa da ta yi da BBC a Legas.
Wane ne Peter Obi?
Mista Obi mai shekara 61, na fatan jam’iyyarsa ta Labour ta shiga sahun manyan jam’iyyun siyasar Najeriya.
Duk da cewa yana cikin PDP ne a da, ana kallonsa a matsayin wani mutum da zai iya kawo sababbin dabaru, kuma yana da goyon baya daga wani ɓangare na matasa, musamman a kudancin ƙasar.
Ɗan takarar ya kasance attajirin ɗan kasuwa, kuma ya taɓa riƙe muƙamin gwamnan jihar Ananbra daga 2006 zuwa 2014.
Magoya bayansa, waɗanda aka fi sani da “OBIdients” na cewa shi ne kaɗai ɗan takara mai nagarta, amma masu adawa da shi na cewa zaɓensa asarar ƙuri’a ce kawai domin ba zai iya lashe zaɓen ba.
Wane ne Atiku Abubakar?
Sai dai a maimakon haka, jam’iyyar PDP wadda ta mulki Najeeriya har zuwa 205, na son ‘yan ƙasar su zaɓi Atiku Abubakar ɗan kasuwa mai shekara 76.
Atiku shi ne ɗan takara ɗaya tilo da ya fito daga yankln arewacin ƙasar wanda akasarin al’ummar yankin Musulmai ne.
Ya taɓa tsayawa takarar shugaban ƙasa har sau biyar a baya – inda bai yi nasara ba a dukkan waɗan nan lokutan.
An dai daɗe ana tuhumarsa da aikata laifukan cin hanci da rashawa da kuma karkatar da arziƙin ƙasa domin amfanin na kusa da shi, tuhumar da ya daɗe yana musantawa.
Yawancin rayuwarsa ta aiki ya shafe ta ne a cikin gwamnati, inda yayi aiki a matsayin mataimakin shugaban ƙasa da babban jami’in gwamnati da kuma shahararren ɗan kasuwa.
Wane ne Rabiu Musa Kwankwaso?
Rabiu Musa Kwankwaso, dan siyasa mai shekara 66 ne da ke takarar neman zama shugaban Najeriya na gaba. Ba kasafai akan gan shi babu jar hula a kansa ba.
Wannan hula alama ce ta kudurinsa da kuma abubuan da ya cimma a rayuarsa ta siyasa – ya kasance tsohon ministan tsaro, kuma ya rike mukaman sanata da na gwamnan jihar kano har sau biyu.
Mabiyansa na rika sanya wadannan jajayen hulunan, musamman a Kano, inda suka kasance cikin wata kungiyarsa mai suna Kwankwasiyya.
Wannan kungiyar ta rika binsa har zuwa wasu jam’iyyun da ya koma – misali komawarsa jam’iyyar APC daga Jam’iyyar PDP mai mulkin kasar a 2013.
Cikin rayuwarsa ta siyasa, Kwankwaso ya shiga jam’iyyu biyar, kuma a yanzu shi ne dan takarar mukamin shugaban kasa a jam’iyyar NNPP (New Nigeria People’s Party), wadda ba a san ta ba sai bayan da ya koma cikinta a bara.
Masu nazarin siyasa na cewa da wuya ya iya lashe zaben shugaban kasa kai tsaye, ganin cewa yawancin masu goyon bayan nasa na arewacin kasar ne, sai dai zai iya zama karfen kafa ta hanyar hana manyan ‘yan takara biyu – Bola Tinubu na jam’iyyar APC da Atiku Abubakar na babbar jam’iyyar adawa ta PDP.
Wane ne Bola Tinubu?
Yawancin mutane na kallon wannan zaɓen a matsayin ma’aunin farin jinin jam’iyyar APC, wadda a ƙarkashin mulkinta ‘yan Najeriya sun fuskanci matsalolin tattalin arziƙi da lalacewar yanayin tsaro.
Ɗan takarar jam’iyyar shi ne Bola Ahmed Tinubu mai shekara 70, wanda ake kallo a matsayin wanda ya raya yankin kasuwanci na Legas a lokacin da ya zama gwamnan jihar zuwa 2007.
Ana kuma kallonsa a matsayin uban gida na siyasa a yankin kudu maso yammacin ƙasar, inda yake da ƙarfin fada-a-ji, sai dai kamar Atiku Abubakar, shi ma ana tuhumarsa da cin hanci da rashawa baya ga rashin cikakkiyar lafiya, tuhume-tuhume da ya dade yana musantawa.
Ana sa ran fara wannan zaben da karfe 8:30 agogon Najeriya, sai dai za a kyale duk wanda ke kan layi yayi zaɓe har bayan lokacin da za a daina zaɓen, wato zuwa karfe 2:30.
Za a kuma yi zaɓuka a mazaɓu 109 na ‘yan majalisar dattawa da na mambobin majalisar wakiliai 360, amma zaben gwamnonin jihohi da majalisunsu, sai cikin watan Maris.
Za a ƙaddamar da wata na’urar zaɓe wadda za ta tantance fuskar mai zaɓen da yatsunsa.
Hukumar zaben ta yi alƙawarin gudanar da zaɓe mai sahihanci.
Wannan ne karon farko da za a yi amfani da na’urar mai suna Bimodal Voter Accreditation System (BVAS), wanda ake ganin zai hana ‘yan siyasa yin maguɗin zaɓe.
A baya dai, an riƙa bayyan sakamakon zaɓukan shugaban kasa a rana ta uku bayan an kammala kaɗa ƙuri’un, sai dai a wannan karon, akwai yiwuwar samun sakamakon kafin rana ta ukun saboda na’urar ta BVAS, wadda aka haɗa ta kai tsaye da shafin hukumar na intanet domin wallafa sakamakon zaɓen daga mazaɓu kai-tsaye.
Tilas dan takarar da ke son lashe zaɓen ya sami aƙalla kashi 25 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa a kashi 1 cikin uku na dukkan jihohin Najeriya 36.
Idan ba a sami haka ba, to za a gudanar da zagaye na biyu na zaɓen cikin kwana 21 – wanda zai kasance na farko a tarihin Najeriya idan hakan ya auku.