Wata mata mai suna Mercy, wacce muryarta ke yawo kan dandazon matan da ta gani a dakinta, tace ta sha matukar wahalar namiji.
Mercy ta bayyana cewa, wannan muryar da ta zama abun dariya ga jama’a, ta fito ne cike da kunar rai tare da takaici Jama’a da dama sun jajanta mata tare da nuna tausayinta a fili kan abinda take fuskanta a aurenta mai cike da cin amana.
Matar dake da muryar nan da ‘yan kafar sada zumuntar zamani ke ta hawa wacce ke bayyana “dandazon mata cike da dakinta” ta bada labari a sabon bidiyo.
Idan za mu tuna, bidiyon ya yadu a cikin kwanakin nan inda take bayyana yadda mijin ta ya kwaso karuwai ya cika mata daki da su suna ta badala.
Duk da mutane sun ga cewa, matar tana bayanin ne a gaban kotu yayin da take korafi kan tsagwaron cin amana da neman mata irin na mijinta, sun dauka abun da nishadi.
Matar tace ta yi fama da bacin rai matuka a auren ta.
A sabon bidiyo da ta saki, Mercy ta sanar da mutane cewa yin amfani da muryar ta wurin nishadi ya matukar bata mata rai.
Ta kara da cewa, fahimtar abinda take fuskanta a auren ta zai tabbatar wa da jama’a cewa ba abun dariya bane.
Mercy tace lamarin da ta fuskanta ya kai kololuwar tsanani, ikon Ubangiji ne yasa ta jure. Ta kuma mika godiya ga wadanda suka tuntubeta tare da bata baki.
Jama’a sun yi martani Legit.ng ta tattaro muku wasu daga cikin martanin jama’a.
“Mugun halin mijinki ya bayyana rabon ki kai tsaye. Komai da kika gani ‘dan hakuri ne.”
Love_marvell tace: “Wannan wace irin rayuwa ce? Aure a gaskiya bashi da sauki. Ina miki fatan alheri mamana.”
Borasiam tace: “Mace na kuka da idanunta kan abinda ta fuskanta amma kuna nan zaune kuma zolayarta.”
Favour/Ivy tace: “Idan kina walwala da farinniki a rayuwar auren ki, a gaskiya kina da sa’a.”
Budurwa ta haifo yaro ba tare da kwanciya da namiji ba, ta yi bayani dalla-dalla.
A wani labari na daban, wata mata mai suna Aba tayi ikirarin cewa ta dauka ciki kuma ta haihu ba tare da ta sadu da namiji ba.
Yayin zantawa da Barima Kaakyire Agyemang a step 1 TV, Aba tayi ikirarin cewa shekara hudu rabonta da kwanciya da namiji. Kamar yadda tace, lokacin da ta fara fuskantar wani irin ciwon ciki da kumburi, tace tayi tunanin cutar fibroid ce.