Kamar yadda labarai suke ishe mu shine an samu matsayar aiki da abinda jagoran harkan musulunci a najeriya, malam Ibrahim Zakzaky ya bada umarni na cewa ayi aiki tare.
A zaman da aka gudanar karkashin jagorancin sharif muhammad jakara an samu matsayar cewa almajiran malam zakzaky na garin kanio zasu marawa duk shirye shiryen da da’iratul amm, ma’ana ”joint fora” wadanda malam zakzaky ya dorawa nauyin aiwatar duk wasu munasabobi na wannan harka din.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yan uwa almajiran malam zakzaky na kano sun samu matsayar kuma sun shirya tsaf domin bin samun sauran ‘yan uwan su na sauran kasashe a wannan babbar ibada.
Tattaki a najeriya dai an soma shi shekaru fiye da goma da suka gabata kuma ya samu karbuwa a wajen jagoran harkar musulunci malam zakzaky dama sauran al’ummar najeriya.
A tarihin tattaki ba za’a mance da gwaraza irin su marigayi sheikh muhammad mahmud turi ba, wanda kafin ya sojoji su harbe shi a waqi’ar zariya shine yake jan ragamar almajiran malam zakzaky na kano tun daga masallachin fagge na kano har zuwa zariya a munasabar tattakin.
Bana ana sa ran wakilin ‘yan uwa almajiran malam zakzaky na kano Dakta Sunusi Abdulkadir kano shine zai jagoranci kanawan domin gabatar da tattakin bana din.
Duk da wasu da aka samu suka ware gefe guda da sunan zasu gudanar da nasu tattakin amma hakan bai ragewa tattakin na bana armashi ba domin alamu na nuna kamar kowacce shekara bana ma kanawan zasu ba mara da kunya kuma zasu amsa kiran Imam Husssain (S.a), kamar yadda takwarorin su na duniya suka amsa.
Kasar saudiyya dai bata son wannan mjunasabobi na ashura da ake rayawa duk shekara kuma ma har ta kan yi kokarin hayar ‘yan isakan gari somin su afkawa wadannan taruka amma duk da hakan almajiran na malam zakzaky basuyin kasa a gwuiwa kuma ana sa ran za’a fara dakile wadancan ayyuka da kasar saudiyya keyin kutse tana sanyawa ana aikatawa.