Yayin da aka gab da shiga bukuwan kirsimeti da na sabuwar shekara wanda a irin wannan lokacin ya kamata a ce, mutane sun wadata da abinci, yadda za a gudanar da wadannan bukuwa cikin yalwa da taiamaka wa marasa karfi, amma sai ga shi, a wannan lokacin alamu na nuna cewa, hakan da kamar wuya, saboda matsalolin tashin farashin gwauron zabon da kayan abincin ya yi.
Kayan abinci irin su shinkafa da mai da kaji da kayan miya da kayan kyale-kyale da ake ado da su a irin wannan lokaci domin nuna farin-ciki da annashuwa, yanzu haka wadannan kayan sun fi karfin talaka.
‘Yansanda Sun Cafke Mutum 9 Da Ake Zargi Da Kai Wa Tawagar Atiku Hari A Borno
An Kammala Kashin Farko Na Layin Dogon Jihar Lagos
Sai dai, a binciken da aka yi a wasu manyan kasuwannin Binin, wato babban birnin jihar Edo, ya nuna cewa, hakan ta faru ne, saboda gwamnati ba ta sa idi kan yadda ‘yan kasuwa ke sayar da kayansu.
Farashin shinkafar gida da ta waje duk ya tashi. Misali, buhun shinkafa mai nauyin kilgiram 50 a kasuwar Oba a da ana sayar da ita naira 40, 000 amma yanzu ta koma naira dubu 50, 000.
Wata mata mai suna Mary-Jane Eche, da ke sana’ar kwalliya a uunguwar Upper Mission a Binin ta ce farashin kayan abinci a kasuwanni ya yi tashin da ’yan Nijeriya da yawa ba za su iya saya ba. Ta ce, farashin abinci ma fi sauki ga dan Nijeriya kamar shinkafa da makamantanta duk farashinsu ya tashi.
Labarai Masu Nasaba
Fara Raba Muhimman Kayayyakin Zabe Da Kone-konen Ofishoshin INEC: Ga Koshi Ga Kwanan Yunwa
Samar Da Cikakkun Cibiyoyin Kiwon Lafiya Ga Al’ummar Duniya
“Ganin yadda abubuwa ke tafiya a halin yanzu, Ba zan iya tafiye-tafiye ba a wannan shekara ba, saboda tsadar mota. Saboda haka, ina kira ga gwamnati da ta kawo karshen wadannan wahalhalu da talakawa ke ciki” In ji ta.
Wani mazaunin jihar mai suna, Mista Solomon Okoduwa, wanda kuma ya bar aiki, yake kuma fuskantar kalubalen rayuwa ya ce, zai yi bikin kirsimetin ne da na sabuwar shekara da dan abin da ya samu daga iyalansa.
“Zan fuskanci kalubalen da ke bikin kamar yadda sauran Kiristoci za su fuskanta. Fatanmu shi ne, Allah ya ba mu lafiya.
Duk da wadannan koke-kike da ake yi na matsin tattalin arziki, da zai tauye hada-hadar kirdimetin bana, da yake an Allah daya gari bamban, su kuwa Kiristan da ke jihar Kwara, snana sai shirye-shirye suke da caba ado da gudanar da bukukwa a lokacin bikin Kirsimetin.
Wasu daga cikin Kiristan da suka tattauna da jaridar LEADERSHIP a Ilorin, babban birnin, sun ce, sun shirya yin bukukuwan Kirsimeti, duk da matsin lambar tattalin arzikin da ake ciki.
Mista Kole Agbede da ke unguwar Sabo-Oke, Ilorin wanda iyalinsa ke zaune a jihar Ekiti, ya ce: “Kirsimeti kan sau daya ne kawai a shekara, saboda haka zan dage in ga na ziyarci ‘yan uwana da ke gida a wannan lokaci. Haka ne, tabbas akwai matsin tattalin arziki, amma duk da haka zan yi kokarin ganin na yi tafiya.”
Another ya ce, Mista Owolabi Amos wanda iyalinsa ke zaune a Ibadan, babban bitrnin jihar Oyo, ya nuna cewa, zai roki Allah ya kawo masa hanyar da zai samun kudin da zai je gida tare da iyalansa domin yin bikin kisimatin. Ya ce, a irin wannan lokacin ne yake samun damar kai wa ‘yan uwansa ziyara.
Shi ma wani lauya mai suna Oladele Moses da ke zaune a Ilorin ya ce,” zuwa yanzu dai babu wani abu da zan ce na shirya domin yin bikin kirsimetin. Za nu yi bikin ne da abin da ya sauwaka a wajenmu.
“Ana cikin matsi a wannan kasa, wanda ya kai ga har mutane ba su san yadda za su yi wannan bukukwa na kirsimetin ba,”in ji Moses.
Wata ‘yarkasuwa mai suna, Misis Kemi Olowo, cewa ta yi, “abin da zan iya cewa shi ne, muna fatan gwamnati ta sassauto da wasu abubuwa, domin mu samu damar yin bukukuwan kirsimetin cikin walwala da annashuwa.
Ta bayyana yashin farashin gwauron zabon da kananzir da gas suka yi cewa, zai kawo tarnaki ga magidanta wajen gudanar da bukukuwan na kirsimeti.
Mazauna Osun ba za su samu cikakkiyar walwala ba, a wannan kirsimetin, saboda tsadar kayayyaki da kuma tsadar kudin mota wanda karancin mai ya haifar da shi.
Wadannan bayanan sun biyo bayan tattaunawar da waikilinmu ya yi ne da wasu mutane kan shirin da suke yi don yin bukukuwan kirsimeti a jihar Osun.
Ita ma da take magana a Osogbo, babban birnin jihar, Misis Janet Alonge, ta ce, dan uwan babansu ya saba kawo musu kaya duk shekara, ammam a bana bai kawo musu komai ba, saboda matsin tattalin arzikin.
Ta ce, ita kanta, saboda tsadar rayuwa ba za ta iya saya wa ‘ya’yanta sababbin kaya ba, da za su sa a wannan kirsimetin ba, ta ce, abinci kawai za ta iya yi saboda shi ya zama dole.
Shi kewa, Mista Emeka Irahbo rukn gwamnati ya yi da ta gaggauta kawo dauki domin samun sassauci daga cikin wannan mawuyacin hali da aka shiga a fadin kasar nan wanda ya ce, shi kansa abin ya shafe shi tare da iyalinsa.
Yanzu haka dai ‘yan kwanakin da suka rage, domin gudanar da bikin kirsimeti da na sabuwar bshekara ta 2022, mutanen jihar kiti na ci gaba da shirye-shiryen bukukuwan duk da cewa, suna kukan maysin tattalin arziki.
Duk da haka an ga mutane na tururuwar zuwa kasuwa a Ado Ekiti, musamman a kasuwar Okesa da da King da Irona da Bisi suna sayen kayan abinci da na sa wa.
Haka ma a Ikere da Ikole da Oye da Ijero da Efon da kuma wasu manyan garuruwa da ke fadin jihar.
Sai dai wani danjarida da ya ziyarci wasu kasuwannin ya ce, a wasau wuraren farashin kayan bai tashi ba.
Ana sayar da da robar gari daga naira 250 zuwa naira 350, ana sayar da kilon nama daga naira 2500 zuwa naira 2,500 sai karamar kwalbar man gyada daga naira 650 zuwa naira 800.
Wani mutum mai suna, Ayodele Owolabi da ya zanta da jaridar LEADERSHIP ya ce farashin kayan abinci da sauran wasu kayayyaki a kan samu tashin farashin kayayyaki a irin wannan lokacin a kowace shekara.
“Ba mu taba samun tashin farashinkayayyaki Kaman wannan karon ba, ga shi kuma kudi na wahala. Amma duk da haka, hakan nan za mu yi bikin kirsimatin da dan abin da ke hannunmu. Mun gode wa Allah da ya kawo mu wannan lokaci”.
Owolabi ya ce, yana so ya kai ziyara zuwa Abuja saboda abokinsa ya gayyace shi amma ba zai je ba, saboda matsalar tsaro.
“Muna fatan gwamnati da jami’an tsaro za su yi dukkan abin da ya dace, domin kare rayuaka da dukiyar al’ummar kasa, kafi da lokacin sannan kuma da bayan kirsimeti”.
Wata mata mai sayar da kayan abinci a cikin daya daga cikin kasunnain da aka ziyarta mai suna, Misi Funke Adeoye ta ce, yanzu haka babu ciki kamar yadda suka saba a lokutan kirsimeti da na sabuwar shekarar da suka wuce, sai dai fatansu a samu cabji a cikin dan wannan lokacin.
“Mutanen da ke zuwa sayen kaya sun koka kan tsadar kayan abinci, saboda haka yanzu ko wata cikakkiyar riba ba ma samu”.
Wadanda za su je garuruwan domin yin bikin kirsimeti da na sabuwar shekara dole su yi kyakkyawan tanaji.
Dole wadanda da yi tafiyar su yi shiri na musamman saboda matsalar tsaro da kuma tsadar kudin mota.
Wani direban bos da ke daukar fasinja daga Ado Ekiti zuwa Legas mai suna Mista Rafiu Ojo ya ce, suna samun fasinjoji da yawa, a mma duk da haka bas u kai yawan na bara ba.
“Ba mu san me ya sa hakan ta faru ba , sai dai muna fatan kullum yawan fasinjan ya dinga karuwa”.
Da aka tambaye shi ko zai yi tafiya a wannan lokaci, sai Andrew Okon wanda ke yin aiki a jihar, sai ya ce, zai je jihar Anambira domin yin bikin kirsimeti da na sabuwar shekara.
“Duk karshen shekara na kan yi wannan tafiya. Na kan fara shirin wannan tafiya da zarar na dawo”.
A Filato, daga kasuwar Taminos zuwa babbar hanyar Ahmadu Bello Way da kuma wasu kananan kasuwanni da ke cikin garin Jos da Bukuru, sun yi cikar kwari da masu saye da sayarwa.
An samu wannan cinkoson a kasuwannin, duk da cewa, ma’aikata ba sa samun albashinsu a duk wata, sai lokaci, lokaci.
Wakilinmu da ya zagaya kasuwar Jos ya lura cewa farashin kaya yayi tashin gwauron zabo da kashi dari.
A kasuwar terminus Mrs.Rabi Adams ta bayyama wakilinmu duk da farashin kayan sun karu ba tada wani zabin da ya wuce na ta sayi ‘yan wadanda zata iya saye.
Shi yasa ta ja hankalin masu sayen kaya da kada su wuce gona da iri domin a watan Janairu ne yara za su koma makaranta, sun kuma san wata ne mai matsala, idan duk suka kashe kudaden da ke hannunsu, abin zai masu matukar wahala su iya biyan kudin makaranta a watan Janairu.
Amma ga Dachollom Yakubu wadda ta mallaki shagon sayar da kayan sawan zamani na mata a titin Ahmadu Bello da Charity Musa mai sayar da kayan miya ta fadama wakilinmu saboda kudin mota ya karu, ba su da abinda za su yi illa suma su kara farashin saboda ta haka ne kawai za su iya cigaba da tafiyar da harkar ba tare da jarinsu ya ja baya ba.Domin kuwa ba wani dan kasuwan da zai so ace yasu jarinsa ya ja baya.
A tashar Plateau Riders data NTAkudin mota sun karu da kashi dari, hakan ta kasance ne saboda karin fashin mai. A daidai lokacin da ake rubuta wannan rahoton mutabe ‘yan kalilan ne aka gani a tashoshin motar, domin tafiya garuruwansu daban- daban.
Jihar Ribas ma lamarin ya sha bamban
Mazauna Fatakwal babban birnin Jihar Ribas sun bayyana ra’yoyinsu daban- daban akan shiye- shiryen da suka yi na tafiya bikin Kirsimati.
Yayin da wasu mazaunan suke fatan za su yi bikin Kirsimatin kamar yadda suka saba yi, duk kuwa da yake ana fuskantar matsalar tattalin arziki a Nijeriya, su kuma wasu suna ganin su za su yi hakuri da bikin Kirsimatin ne yadda ya same su, wato irin halin rayuwar ds suke ciki.Wasu kuma cewa suka yi za suyi bikin Kirsimati da sabuwar shekarar
Da yake hira da Jaridar LEADERSHI ta Asabar mazaunin gundumar Borokiri a karamar hukumar Fatakwal,Oji Onyeuwa, zai yi kokari don tabbatar da iyalansa sun kasance cikin farinciki lokacin Kirsimati
Onyeuwa yace: “Ka san abubuwa sun yi tsauri amma mun gode ma Allah muna da rai za muyi bikin wannan kirsimati.Don haka zan sayi duk abubuwan dana saba sai ma iayalina lokacin Kirsimati, sai dai na za su iya kasancewa suna da nagartar irin wadanda aka yi amfani da su bukukuwan kirsimatin da suka gabata.
“Kana maganar matsalar tattalin arziki ai yara basu san abinda ake nufi da matsalar tattalin arziki ba, abinda suka sani shine dolene su sa sabbin kaya lokacin Kirsimati, su kuma ci Kaza. a ranar”.
Shi ma wani direban Tashi da yake tattaunawa da Jaridar LEADERSHIP Asabar Udo Humphrey,cewa yayi yana farinciki tunda yana raye, ya samu yin bikin wani Kirsimatin, zai yi iyakar kokarinsa bikin ya kasance ma shi maikyau a wannan lokacin.
Humphrey ya cigaba da maganar cewa “ Tun lokacin daya zo Fatakwal shekara ashirin da suk dasuka wuce bai taba fasshin zuwa gida bikin Kirsimati ba, zuwa garinsu da yake JiharAkwa Ibom ba. Amma wannan shekarar babu kudi ko ina, don haka zai tsaya da iyalansa a Fatakwal wannan Kirsimatin, za su ci duk abinda za su iya saye abincin da kudin da suke dasu su ci.
Anata banagaren wata mace ‘yar kasuwa, a kasuwar hanyar Creek a Fatakwal Bictoria Ndukwu, ta ce hauhawar farashin kayan abinci, yasa abin ya zama mata dole ga iyalanta su yi bikin Kirsimati kamar yadda suke fatan yi.
Tace“Dubi farashin buhun shinkafa ta yaya iyalai za su iya sayen shi Naira 40,000 a sayi buhu daya saboda Kirsimati wannan ba maganar aba wasu mutane?
“Zan je kauyenmu in ga Kakanni na wadanda ban gani ba ku san wata shida yanzu, amma na fada masu kada su san ran zan kawo masu abinda na saba kawowa ba lokacin Kirsimati saboda al’amarin rayuwa yayi matukar tsauri.
Shi kuma Abayomi Babalola, dan asalin Jihar Oyo ne amma mazaunin Jihar Sakkwato, yace bikin Kirsimatin wannan shekarar shi ne na farko wanda zai yi a Sakkwato a shekarun sa biyar da zama a Jihar Sakkwato.
Yace“ Tun lokacin da yazo shirin aikin yi ma kasa hidimako aikin bautar kasa shekaru biyar da suka gabata har yanzu da naka matsayinma’aikaci, babu wani bikin addini da nayi a Sakkwato, saboda shi a iyalansu suna da Musulmi da kuma Kirista.
Yace“lokacin bai da wasu al’amuran da suka shafi kudi da suka dame shi, ba kamar yanzu ba, da naked a mata wadda ta dogara dani wajen kulawarta. Karin kudin mota kadai ya sa na sauya abinda nayi shirin yi, in tsaya nan Sakkwato na ga yadda suke yin bikin Kirsimati
Yace “Na tattauna maganar da matata mun yanke shawarar zamu tsaya Sakkwato mu yi bikin Kirsimati, saboda muna kashe kudi da yawa a matsayin na mota lokacin da muka je gida tare da Babbar Sallah.
“Akwai karin kudin mota zuwa da dawowa gida, wannan kuwa saboda karuwar fasinjoji wadanda suke zuwa gida. Don haka dole ne yanzu mutum yayi tunanin nawa kudin motar zasu kasance domin kuwa ai farashin man fetur ya karu.”
Lokacin da LEADERSHIP ta Asabar ta binciki babbar tashar motar Sakkwato kudin mota bdaga Sakkwato zuwa Ibadan dubu goma sha daya ne.
Sai dai kuma wani dan kungiyar direbobi ta kasa rashen Jihar ya ce akwai yiyuwar farashin ya canza a ‘yan kwanaki masu zuwa, saboda yawan masu son su tafi gida bikin Kirsimati.
Halin Da ake ciki Kaduna kan farashin mota
Mrs Dorathy Ejimatswa cewa tayi, “ na so in yi tafiya amma dana tambayi kudin motar, sai naji abin ba zai iya jure biyan hakan ba don haka ba zan yi tafiya ba, har sai lokacin da al’amarin ya gyaru.
“Maganar Kirsimatin wannan shekarar ba wata tafiyar da zan yi, kudin mota daga 4000 sun koma zuwa 9000, zan tura masu abinda nake da shi maimakon tafiyar”.
Farashin kayan abinci ma shi yafi daure kai yanzu buhun shinkafa daga Naira 50 ko 55,000 ne, lita 5 ta mangyada yanzu Naira 8500.Kaza ma mai dan girma yanzu ana sayar da ita kusan Naira 8000, don haka wannan Kirsimatin zamu yi hakuri ne da abinda za mu iya saye ne anan”.
Shima Mista John Andrew cewa yaja da baya kan shiri na tura iyalansa zuwa gida Kogi su yi Kirsimati, amma da yana da niyyar hakan, ya dai bari ne saboda karin kudin mota da aka yi.
Yace “Ba irin wannan muka yi fata a wannan kasa, wannan gwamnati dake kan karaga ta bamu mamaki,duk ta gagara cika alkawuran da tayi, ai abin takaici ne.Yanzu man fetur babu isasshe bama a iya sayen shi wannan shi ya shafi farashin shi aduk indaake kasuwancin sa.
“Ina fatan ‘yan Nijeriya za su sake tunani a shekarar 2023 wajen yin abinda ya kamata lokacin zaben Shugabanni a shekarar 2023,a zabi Shugabanni masu tsoron Allah, irinsu ne za su samar da canjin da Talaka ke bukata.”