Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce matsalar rashin tsaro da Najeriya ke fuskanta na barazanar gurgunta shirin aikewa da jami’an tsaro da albarkatun kasa da kuma yanayin tsaro a kasar.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne jiya Juma’a a Abuja, yayin kaddamar da wani daftari na takaita rikice-rikice ta kasa da nufin cike gibin da aka samu ta hanyar aike da jami’an tsaro masu yawa ta hanyar hadin gwuiwa tsakanin ma’aikatu da hukumomin gwamnati.
Shirin da ofishin mai bai wa shugaban shawara kan harkar tsaro da kuma hadin gwuiwa da hukumomi, zai tabbatar da cewa an samu nasara wajen dakile rikice-rikice a fadin kasar.
Buhari ya tuna cewa a lokacin da gwamnatinsa ta zo kan mulki, Nijeriya na fuskantar matsalolin rashin tsaro da dama kama daga ta’addanci da garkuwa da mutane da fashi da makami da hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi da satar danyen mai da sauransu.
Hakazaila, shugaba Buhari ya jinjinawa mai taimaka masa a bangaren sha’anin tsaro da kuma sauran hukumomi saboda samar da shirin, inda ya ce hakan ya nuna zimmar da ake da ita na ganin an magance matsalar rikice-rikce a fadin kasar.
Sai dai ya koka kan yadda matsalar rashin tsaron ke ci gaba sa zama babbar barazana ga tattalin arzikin kasar da kuma zaman lafiya.
Shugaba Buhari dai shine Shugaban da yayi alkawarin kawo karshen matsalar rashin tsaro.
Amma a gwamnatin sa ne aka fuskanci rashin tsaro mafi tsanani a Najeriya amma zuwa yanzu gwamantin tasa ta kasa karbar gazawar ta dangane da rashin tsaron.
Ana sa ran shekarar 2023 gwamnatin buhari zata gama wa’adin ta inda ake sa ran sabuwar gwamnati ta karbi gabarar gudanarwa a Najeriya idan anyi sa’a gwamnatin mai kamawa ta iya kawo hanyar magance matsalar Tsaro amma zuwa yanzu ‘yan Najeriya sun fidda tsammani daga gwamnatin buhari wacce ya rage mata ‘yan watanni ta sauka.
Source: ABNA