Matsalar tsaro na ƙara ta’azzara a jihar Sokoto
Ga mafi yawan mutanen yankin, matsalar tsaro a yankin Arewa maso yammacin Najeriya ba sabon al’amari bane.
Saboda daɗewar da yankin ya yi yana fama da ita, da kuma yadda take faruwa a kai a kai.
Sai dai ko a yankin akwai wurin da ya fi wani muni, akwai kuma inda ya fi sassauci idan an kwatanta da sauran yankuna.
Jihar Sokoto na daga cikin jihohin da wannan matsala ta tsaro ta zamar wa alaƙaƙai. A kusannan kuma yankin gabashin jihar ne abun ya sako a gaba.
Ko a kwanakin baya sai da aka kashe mutum huɗu a wani harin ‘yan bindiga suka kuma sace sama da mutum 30 a lokaci guda.
An ɗauki kwanaki ba a ji komai daga wurin ‘yan bindigar ba, kamar tattaunawar nawa za a biya kan mutanen a matsayin kuɗin fansa, abin da ya sanya al’ummar yankin neman taimakon hukumomi domin dawo masu da ‘yan uwansu gida.
Senata Ibrahim Lamido shi ne dan majalisar dattawa mai wakiltar shiyyar, kuma a wata tattaunawarsa da BBC ya ce “babu wata ƙaramar hukuma a gashin Sokoto da ba ta fama da matsalar ‘yan bindiga.”
Ya bayyana abin da ke faruwa a yanzu a yankin a matsayin abin takaici da baƙinciki.
“Babu ƙaramar hukumar mulki guda da zan ce maka ba su samun wadannan matsaloli, sai dai akwai inda kila inda ya fi sauƙi.
“Amma irin su Goronyo da Isa da Sabon Birnin da Raba da Gwadabawa da kuma Illela sai dai a sanya a addu’a,” in ji Sanata Ibrahim Lamido.
Sanatan mai wakiltar Gabashin Sokoto ya ce “ban san adadin ƙauyukan da ‘yan bindiga suka tasa ba a ƙananan hukumomi takwas da ke Gabashin Sokoto inda nake wakilta”.
Da aka tambaye shi batun jami’an tsaro da ke yankin, waɗanda mutane ke cewa kamar “babu su” sai ya ce sun yi kaɗan ne.
“Jami’an tsaron da ke yankin sun yi kaɗan. Idan wani abu ya faru a wannan ƙauyen sun zo sai ‘yan bindigar su sake tafiya inda jami’an suka baro ko kuma wani ƙauyen na daban”.
Wannan ta sa Sanata Ibrahim Lamiɗo ya ce za su nemi a ƙara yawan jami’an tsaron da ke yankin.
Ya ce suna ta bullo da shirye-shiryen da za su aiwatar domin haɗa kai da jama’ar gari wajen kawo ƙarshen wannan matsala.