MATSALAR MAN FETUR: Ƙungiyar Ƙwadago ta TUC za ta tafi yajin aiki.
Daga Tukur Sani Kwasara
Kungiyar Ƙwadago ta Kasa sun yi barazanar tafiya yajin aiki akan matsalar ƙarancin fetur ta ci gaba nan da ‘yan kwanaki kaɗan nan gaba.
TUC ta bayar da wannan sanarwa ce a ranar Lahadi ta bakin Babban Ma’ajin ƙungiyar na ƙasa, Mohammad Yunusa, a wurin taron Manyan Jami’an Kamfanoni Masu Zaman Kan Su Da Manyan Jami’an Kamfanonin Gwamnati.
Matsalar ƙarancin mai ta faru ne daga lokacin da aka gano cewa an shigo da gurɓataccen fetur a cikin Najeriya, kuma tuni ya shiga hannun kwastomomi.
Hakan ya kawo ƙarancin fetur a gidajen mai. Inda ke da fetur ɗin kuma su na tsawwala tsada, sannan gurɓataccen ya lalata motoci da yawan gaske.
Biranen Abuja da Kano da Legas ne aka fi wahalar fetur ɗin. Amma a yanzu lamarin ya yi nisa a wasu garuruwa da daman gaske.
Duk da NNPC ya bayyana cewa matsalar fetur za ta gushe, domin nan da ƙarshen watan Fabrairu za a shigo da lita sama da biliyan 2.1.
Sai dai kuma duk da haka, ƙungiyar TUC ta shaida cewa, “Kwanan nan zasu tafi yajin aiki idan har matsalar fetur ta ci gaba a faɗin ƙasar nan.” Haka Mohammed Yunusa ya bayyana.
“Kuma mu na kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙara miƙewa tsaye domin a gano masu hannu wajen haddasa wannan matsalar fetur ɗin.
“Matsayin ƙungiyar TUC a fili ya ke tun cewa tilas a zaƙulo masu hannu daga
wajen shigo da gurɓataccen fetur ɗin tilas a gano su a hukunta su.
“Matsayar da SSAS da CGOC su ka ɗauka cewa ma’aikata su daina shan wahalar zuwa wurin aiki har sai fetur ya wadata tukunna.”