Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawale, ya bada tallafin kudi naira miliyan 200 don sayo Shanu da Ragunan Layya da rabon tsabar kudi ga mutane daban-daban a jihar don saukaka musu da basu damar samun yin Layya.
Sakataren yada labaran Jam’iyyar APC a jihar, Yusuf Idrisa Gusau, ne ya sanar da hakan a wata sanarwar menema labarai da ya fitar a Gusau a karshen mako.
Matawalle, wanda yake daya daga cikin Jagororin jam’iyyar APC a jihar, ya umarci shugabannin jam’iyyar APC na jihar karkashin shugabanta, Hon. Tukur Umar Danfulani, da ya jagoranci rabon Shanun da Ragunan layyar.
Wadanda za su ci gajiyar rabon sun hada da ‘Yan Jam’iyyar APC, marayu da marasa galihu da malaman addinin Musulunci da dai sauransu.
Shugaban jam’iyyar ya mika godiyarsa ga tsohon Gwamna, Bello Matawallen, kan wannan karamcin da ya yi wa al’umar Jihar Zamfara.
A wani labarin na daban gwamnatin jihar Katsina ta bayar da hutun mako guda ga daliban makarantun Firamare da Sakandare domin gudanar da bukukuwan sallar idin layya a jihar.
Sanarwar na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun mukaddashin babban sakataren ma’aikatar ilimi, Ya’u Jibrin, wadda jaridar LEADERSHIP ta samu kwafinta a ranar Lahadi.
“An ba da wannan hutun ne na mako guda ga daukacin Makarantun Gwamnati da masu zaman kansu a fadin Jihar daga ranar Litinin 26 ga watan Yuni zuwa Litinin 3 ga Yuli, 2023,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa, ana sa ran daliban makarantar kwana za su koma makarantun su a ranar Lahadi 2 ga Yuli, 2023.
Sabida haka, ma’aikatar ilimi ta na yi wa daukacin ma’aikata da dalibai barka da Sallah.