Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ce, sabuwar matatar man da Dangote da aka kaddamar za ta taimakawa Nijeriya wajen samar da karin wutar lantarki.
Da yake jawabi ranar Litinin a wajen kaddamar da aikin da ke yankin Ibeju-Lekki a jihar Legas, gwamnan babban bankin kasar, Godwin Emefiele, ya ce matatar Dangote za ta samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 12,000.
Emefiele, wanda ya ce, a lokacin da aka fara aiwatar da aikin, an kiyasta cewa za a kashe kimanin dalar Amurka biliyan 9, daga cikin dala biliyan 3 da aka yi hasashen za a yi a matsayin hannun jarin da Rukunin Dangote da kuma abunda da aka samu ta hanyar rancen kasuwanci, ya yaba da rawar da bankunan kasuwancin Nijeriya ke takawa. domin bayar da lamuni ga rukunin Dangote domin gudanar da aikin.
Ya bayyana godiya ta musamman ga dukkan bankunan cikin gida Nijeriya, wadanda suka ba da tallafi mai yawa.
Bugu da kari, ya bayyana cewa tuni Dangote ya fara biyan wasu lamunin kasuwanci kafin kaddamar da cibiyar, duk da cewa ya bayyana cewa bashin da ake bin rukunin Dangote ya ragu daga dalar Amurka biliyan 9 zuwa dalar Amurka biliyan 2.7. .
Idan aka yi la’akari da yadda ake sarrafa gangar mai 650,000 a kowace rana (BPD), Gwamnan CBN ya ce matatar ta fi karfin dukkan man da Nijeriya ke amfani da shi a cikin gida, wanda ya kai kusan ganga 450,000 a kowace rana, yayin da za a samu rarar man da ake hakowa da za a iya fitarwa.