Rundunar ‘yansandan Jihar Kano, ta kama mataashin da ake zargi da cinna wa wani masallaci wuta, yayin da mutane ke tsaka da sallar Asuba.
Lamarin da ya faru a garin Larabar Abasawa da ke Karamar Hukumar Gezawa a Jihar, ya jikkata mutane da dama.
Cikin wata sanarwar da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce mataashin mai suna Shafi’u Abubakar mai shekaru 38 ya shiga hannunsu bayan wani bincike da suka gudanar.
Hukumomin bayar da agaji a jihar sun mika akalla mutane 24 Asibitin Koyarwa na Murtala Muhammad da ke jihar, inda ake jinyar su.
A gefe guda kuma wata majiya ta ce tuni mutum daya ya riga mu gidan gaskiya sakamakon munanan raunuka da ya samu sakamakon kunar wuta.
Shaida a garin sun bayyana cewar matashin ya yi amfani da man fetur wajen kunna wutar, bayan ya rufe masallata ta wajen masallacin.
Kakakin ya ce binciken farko da suka gudanar a kan matashin, ya ce ya dauki matakin ne sakamakon gaza raba musu gadonsu da aka yi.
DUBA NAN: Jam’iyyar APC Tazo Ne Domin Talakawan Adamawa
A cewar matashin wadanda suka hana rabon gadon suna Masallacin a lokacin da ake sallar Asuba, wanda hakan ya sanya ya yanke hukuncin daukar matakin.
A wani labarin na daban Hukumar Aikin Hajji da Umarah ta Kasar Saudiyya ta gabatar da wasu kundaye 15 da za su taimaka wajen yi wa alhazai jagoranci da wayar da kai a kan aikin Hajji daga ko ina a fadin duniya, a shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin bana a kasa mai tsarki.
Wannan ci gaba na daga cikin tsare-tsaren da hukumar ta gabatar domin wayar da kan al’umma a yayin aikin hajjin bana na shekarar 1445 bayan hijira wanda ya yi daidai da 2024.
Hukumar ta sanar da hakan ne a shafukanta na kafofin sada zumunta da kuma shafinta na Intanet: https://guide.haj.gov.sa/