Lauyan Aminu Adamu, K Agu yace matashin da yake tsare a kurkuku yana da jarrabawa a gaban sa.
Adamu yana gidan gyaran hali a lokacin da sauran abokan karatun sa suke shirin jarrabawar karshe.
A dalilin wannan ne Lauya da sauran mutane suke rokon a fito da wannan yaro domin ya karasa digiri.
K Agu wanda shi ne Lauyan da ya tsayawa Aminu Adamu a kotu, ya bayyana cewa ya nemi ‘yan sanda su bada beli saboda uzurin jarrabawa.
Daily Trust ta rahoto K Agu a ranar Laraba, 30 ga watan Nuwamba 2022 yana cewa Aminu Adamu zai fara jarrabawa a ranar 5 ga watan Disamban nan.
Idan matashin ya samu beli, zai iya zana jarrabawarsa ta karshe a jami’ar tarayya ta garin Dutse. Idan bai samu ba, akwai yiwuwar yayi asarar shekara.
Lauyan da ya tsayawa dalibin jami’ar ya shaidawa manema labarai cewa tun ranar Juma’a ya nemi a bada beli, amma hukuma ba tace masa uffan ba tukuna.
Muna jiran ‘yan sanda – Lauya “Ko a zaman kotun jiya, mun fadawa Alkali mun bukaci ‘yan sanda su ba Aminu beli a kan lokaci, amma ba su ba mu amsar ko za suyi ba.
Saboda haka muka bukaci kotu ta ba shi beli saboda larurar rashin lafiya kuma zai fara jarrabawar makaranta a ranar 5 ga watan Disamba.
Kuma yanzu kotu ta bada umarni ga ‘yan sanda su gabatar da takardar neman belin da muka shigar saboda ayi aiki a kai, a yau ko gobe. – K. Agu
Lauya yace tun jiya aka kai shi kotu Abba Hikima wanda Lauya ne mai kare hakkin mutane ya tabbatar da wannan labarin, yace tun a ranar Talatar nan aka gurfanar da Aminu Adamu.
Lauyan yake cewa abin da mafi yawan mutane ba su sani ba, tun a jiya aka aika matashin gidan gyaran hali duk da jarrabawar jami’a tana gabansa.
Za a batawa yaro rayuwarsa! Shi kuma Dr. Aliyu Isa Aliyu, wanda malami ne a jami’ar tarayyar da Aminu yake karatu, ya yi magana a shafin Facebook, yace za a lalata rayuwar yaron.
Aliyu Isa Aliyu yace idan matashin bai rubuta jarrabawarsa ba, ba zai samu damar kammala karatun jami’a da wuri ba, an yi asarar karatun tsawon kenan. Ba rabo da gwani ba…
A wani rahoto, kun ji an yi lokacin da mutanen kasar nan suka rika cin mutuncin Shugaba, Dr. Goodluck Jonathan da uwargidarsa, Patience Jonathan.
Sai ga shi wasu mutane a Twitter suna cewa sun gane kuskurensa wajen sukar Goodluck Jonathan, har suna yi wa tsohon shugaban addu’ar musulunta.
Source:Legithausa