Rayuwar wani matashi mai kafa daya na gab da canjawa bayan kokarinsa ya ja hankalin shugaban cocin OPM Apostle Chibuzor Gift Chinyere.
An dauki bidiyon matashin wanda ya bar makaranta yana aiki a wajen gini da taimakon sandar guragu kuma hakan ya taba zukata Apostle Chibuzor ya bayyana cewa matashin zai bar kasar don tafiya karatu a waje kyauta.
Cocin Omega Power Ministries (OPM) ya sake ceto wani matashi mai fama da nakasa sannan ya sanya farin ciki a zuciyarsa ta hanyar bashi tallafin karatu a kasar waje.
Bidiyon wani matashi mai kafa daya yana aiki a wajen gini ya yadu a shafukan soshiyal midiya kuma hakan ya burge mutane da dama.
Daya daga cikin wadanda bidiyon ya burge shine shugaban OPM Apostle Chibuzor Gift Chinyere wanda ya bayar da cigiyar mutum ya kuma gano shi.
A Wajen Daurin Aurensa Shugaban OPM ya bayar da karin haske game da lokacin da matashin zai bar kasar Da yake yada sabon hoton mutumin da mabiya shafinsa Facebook a ranar Lahadi, 31 ga watan Yuli, Apostle Chibuzor ya bayyana bakin cikin da ke tattare da labarinsa.
A cewar shugaban na OPM, matashin ya rasa kafarsa ne a wani hatsari a hanyarsa ta zuwa makaranta.
Iyayen sa wadanda suka kasance talakawa sun yi amfani da abun da ya rage masu don ceto rayuwarsa kuma hakan yasa suka rasa kudin ci gaba da tura shi makaranta.
Iyayen na zaune a gidan laka Da wannan tallafin, Apostle Chibuzor ya nuna yakinin cewa wannan matashi zai fitar da iyayensa daga kangin talauci.
Kan lokacin da matashin zai tafi, ya rubuta: “Da izinin Allah, Apostle Chibuzor ya sama masa fasfot daga hukumar kula da shige da fice kuma an fara nema masa takardu da biza.
“Kuma zai shiga sahun dalibai 46 da OPM ya baiwa tallafin zuwa waje yin karatu a watan Agusta.” Jama’a sun yi martani Ekeke Victor ya ce: “Wow Allah ya ci gaba da kareka ya kuma yi maka albarka.”
Harris Eluwah ya ce: “Uban dukka kasa na aiki. Daddy OPM Allah ya albarkace ka da iyalinka. Kana kokari.”
Ezeiruaku Ozzie ya ce: “Wannan abun a yaba ne. “Ina tayaka murna dan uwa CHIBUZOR UCHENDU. “Allah ya tuna ka da alkhairi.
“Allah ya albarkaci uba nagari.” Yadda Matasa 3 Suka Kama Sana’ar Kosai, Sun Mayar Da Hankali Wajen Ganin Sun Yi Kudi, Hotunansu Ya Yadu.
A gefe guda, wani dan Najeriya mai suna Alarma Abd-Karim Isola a Facebook a ranar Laraba, 27 ga watan Yuli, ya je shafinsa don rubuta labarin wasu hazikan matasa uku a Offa.
Ya ce matasan sun bude sana’ar siyar da kosai sannan suka mayar da hankali a kai.
A cewarsa, shekarunsu na a tsakanin 20-25.
Isola ya bayyana cewa matasan wadanda ba yan gari bane sukan kasance cikin kyakkyawan shiga kuma suna faran-faran yayin hulda da abokan cinikinsu.
Ya kara da cewa suna dauke da askin da ake yiwa lakani da na ‘Yan Yahoo’.
Source:hausalegitng