Rundaunar ‘yan sanda ta yi nasarar cafke wani matashi da ake zargin ya daba wa mahaifiyarsa wuka a jihar Kano.
Kakakin rundunar ‘yan sandan a jihar, SP Abdullahi Haruna ne ya sanar da haka a ranar juma’a 5 ga watan Mayu.
‘Ya’yar wanda ake zargin ta ce Ibrahim daman ya na fama da matsalar kwakwalwa, kuma yafi shekara guda ba ya zuwa wurin da suke.
Rundunar ‘yan sanda ta kama wani yaro, Ibrahim Musa da ake zargin ya kashe mahaifiyarsa mai kimanin shekaru 50 a Rimin Kebe cikin karamar hukumar Ungogo da ke jihar Kano.
Kakakin rundunar a jihar, SP Abdullahi Haruna ne ya ba da wannan sanarwar a ranar juma’a 5 ga watan Mayu, Daily Trust ta tattaro.
Wannan matashi da ake zargin an kama shi ne a wata mabuya ta masu aikata munanan laifuka a karamar Hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano.
Rhotanni sun tabbatar cewa wanda ake zargin ya tabbatar da aikata laifin, kuma za a tasa keyarsa zuwa kotu bayan an gama bincike.
Da take bayanin yadda al’amarin ya faru, ‘ya’ayar wanda ake zargin ta ce: “Ya share fiye da shekara guda ba tare da ya zo in da muke ba, kawai sai muka ganshi misalin karfe 5:30 na yamma”.
“Ya na rayuwa ne da mahaifinsa a Kurna bayan ya sha fama da matsalar kwakwalwa, kwatsam sai gashi nan ya shigo gidan ya na tambayar mahaifiyarmu”.
“Da ya tambaya ko tana nan aka ce ta shiga makota sai ya sa aka kirata, ta shigo ta na fara’a da ta ganshi, sai muka ji ta kurma ihu ashe wuka ne a hanunsa”.
“Ni ma ya yi kokarin kaimin hari amma na gudu, a lokacin ne mutane suka kawo mana dauki, shi kuma sai ya jefar da wukan ya gudu”.
‘Ya’yar wanda ake zargin ta kara da cewa: “Marigayiyar ta saba kai masa ziyara duk lokacin da ta yi mummunan mafarki da ya shafe shi, zuwan ta na karshe a watan azumi korar kare ya mata da kyar ta tsira bayan mutane sun kawo mata dauki”.
Source:LegitHausang