Yan sanda a karamar hukumar Mangu na jihar Filato sun kama wani matashi Bernard.
Matashi Danladi dan shekara 25 kan kashe mahaifinsa mai suna Danladi Mangna.
Binciken da yan sanda suka yi ya nuna cewa Bernard Danladi ya yi fada ne da kaninsa Zugumnan.
Danlami sai mahaifinsu ya zabe Bernard Hakan ya fusata Bernard ya tunzura ya dauki dutse ya jefi mahaifinsa a goshi ya masa mummunan rauni da ya yi ajalin sa.
Rundunar yan sanda ta jihar Filato a ranar Juma’a ta tabbatar da kama wani Bernard Danlami, mai shekara 25 kan kashe mahaifinsa a karamar hukumar Mangu, rahoton The Punch.
Kwamishinan yan sandan jihar Filato, Onyeka Bartholomew, ya tabbatarwa manema labarai hakan yayin da ya ke jawabi kan ayyukan hukumar a hedkwatar yan sanda a Jos, ranar Juma’a.
Ya ce: “A ranar 12/05/2022 misalin karfe 6 na yamma, an kawo rahoton kisar gilla a caji ofis na Mangu a ranar 11/05/2022 misalin karfe 9.20 na dare yayin da fada ya kaure tsakanin yan uwa biyu, Bernard Danlami, namiji mai shekaru 25 da Zugumnan Danlami, namiji, dan shekara 18 na Cocin Shamsoho, karamar hukumar Kerang kan bokitin ruwa.
“Amma da mahaifinsu, wani Danladi Mangna, ya dora wa Bernard Danladi laifi saboda rashin da’a ya doke shi da sanda, Benard ya dauki dutse ya buga wa mahaifinsa a goshi, hakan ya yi sanadin rauni mai muni kuma ya yi ajalinsa.”
Wanda ake zargin ya amsa laifinsa Ya cigaba da cewa bayan samun rahoton, sun kama wanda ake zargi sun masa tambayoyi kuma ya amsa aikata laifin, Ripples Nigeria ta rahoto.
Za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike a cewar kwamishinan yan sandan.
Sau 3 Ina Kokarin Kashe Mahaifi Na Don In Gaje Dukiyarsa, Dan Jihar Kano.
A wani rahoton, hukumar yan sanda a jihar Kano ta kama wani matashi da bindiga a unguwar Gadon Kaya da ke cikin birnin jihar Kano, rahoton Daily Trust.
Matashin mai shekaru 25 da haihuwa, Nasir Kabir, ya bayyana abinda yake niyyar yi da bindigar.
Kabir ya shaidawa yan sanda cewa sau uku yana kokarin kashe mahaifinsa don ya gaje dukiyarsa kuma yaji dadi kamar yadda abokansa ke yi.
Source:LEGITHAUSA