Wasu Matasa sun kai hari ofishin ‘Yan Sandan dake Tangaza a Jihar Sokoto inda suka kashe mutane 13 da ake zargin cewar ‘Yan bindiga ne, kana suka kona su da wuta.
Rahotanni sun ce bayan harin, ‘Yan Sanda da ‘Yan Sakai suka hada kai wajen bin sawun ‘Yan bindigar abinda ya basu damar kama 13 daga cikin su.
Labarin tsare Yan bindigar a ofishin ‘Yan Sanda ya harzuka matasa a garin, wadanda suka yi gangami wajen kaiwa ofishin hari da kuma kashe wadanda ake zargin, kana suka kona gawarwakin su.
Mai Magana da yawun ‘Yan Sandan Jihar Sanusi Abubakar ya tabbatar da aukuwar lamarin.
A wani labarin na daban mazauna karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto na rayuwa ne a cikin bakin ciki sakamakon hare-hare, da barnar da ‘yan bindiga ke yi wa kauyen da kauyukan dake makwabtaka da su.
Sakamakon wannan hare-haren dubban mata, yara matasa da tsaffi dake karamar hukumar Sabon Birni sun yi gudun hijira zuwa sakatariyar karamar hukumar, da makarantar firamari na Abdulhamid dake Sabon Birni.
Jaridar Daily Trust ta wallafa labarin dake cewa, da yawa daga cikin wadannan ‘yan Gudun hijiran sun koma Tudun Sunnah a jihar Maradi dake jamhuriyar Nijar, yayin da akwai wasu ‘yan gudun hijiran da yawa, da suka so tafiya kasar ta Nijar, amma baza su samu damar tafiya ba, sabo da wasu dalilai.