Matar tsohon fitaccen mawakin Najeriya Eedris Abdulkareem zata taimaka masa da kodanta saboda lalurar koda da yake fama dashi.
Mawaki MI Abaga ya yi kira ga magoya bayan Eedris da masu hannu da shuni da su taimka masa da kudin da za yi masa tiyatar dashen koda.
Ana sa ran za a yiwa Eedris Abdulkareem dashen koda a karshen watan Yuli.
Wani na kusa da iyalan mawaki Eedris Abdulkareem ya shaida wa jaridar TheCable Lifestyle cewa matar mawakin ta dauki nauyin ba wa mijinta kodarta bayan an kammala yi masa dukkan nau’ikan gwaje-gwaje.
Abdulkareem, tsohon shahararren mawakin Najeriya, yana fama da ciwon koda.
Ana dai yi wa mawakin wankin koda a wani asibiti da ke Jihar Legas kuma ana sa ran za a yi masa dashen koda ne a karshen watan Yuli.
Abin da ya rage a yanzu shi ne a samu adadin kudin da ake bukata don yi masa aikin tiyata,” in ji shi.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da shahararren mawakin gambara MI Abaga, ya yi kira ga magoya bayansa da masu hannu da shuni da su taimakawa mawaki da kudi dan a samu anyi masa aikin tiyatar cutar da yake fama dashi. MI ya kuma bayyana cewa “mun samu mai bada gudummawar koda a cikin danginsa”.