An harbi matar Malamin ne tare da mijin ta Sheikh Ibrahim Zakzaky a Zariya, Jihar Kaduna a ranar 14 ga disambar 2015, kwana biyu bayan sojojin Najeriya sun kashe daruruwan mambobin harkar Musulunci ta Najeriya wadanda aka fi sani da ‘yan Shi’a.
Malama Zeenah Ibrahim, matar Jagoran harkar Musulunci a Najeriya wadanda aka fi sani da ‘yan Shi’a, ta bayyana wahalhalu gami da radadin da ta jure a dalilin harsasan da suke a cikin ta tun wancan lokaci.
Kamar yadda hukumomin kare hakkin bil’adama suka sanar kimamin gawarwaki 300 aka binne a rami.
Malama Zeenah ta bayyana tana fama da mugayen raunuka a cikin ta sakamakon wadancan harsasai.
Ta bayyana hakan a wani taron duniya da aka gudanar a babban birnin tarayyar Abuja ranar asabar.
Zeenah wacce tayi magana ta magiji ta bayyanawa mahalarta taron cewa, bata bacci balle tafiya sakamakon tsananin ciwo dake damun ta.
Kamar yadda ta bayyana, ikon Allah ne kawai yasa take raye zuwa yanzu.
Malamar ta bayyana cewa ” Nasan muna raye ne kawai saboda Allah yana son mu rayu”
Rahotanni dai sun tabbatar da cewa tun bayan abinda ya faru a disambar ta shekarar 2015, Sheikh Zakzaky tare da mai dakin sa sun kasance a hannun hukumomi har lokacin da wata babban kotu a Abuja ta wanke su daga laifin da aka tuhume su da shi.
Amma sai dai bayan fitowar su daga kurkuku zuwa yanzu Basu samu zarafin tafiya kasashe ketare domin neman lafiya kamar yadda suka bukata ba.
Sai dai hakan ba zai rasa nasaba da rashin takardun tafiyar su ba, wanda hakan ke zaman babban tarnakin da ya hana Malamin da mai dakin sa tafiya neman lafiya din.