Kiwon Akuya sannnen abu ne a kasar nan, wanda kuma yake taimaka wa tattalin arzkin kasar nan wajen samar da kudin shiga.
Ana kuma kara samun bukatar naman awaki, musamman a tsakanin gidajen sayar da abinci da kuma a otel-otel.
Irin yanayin Nijeriya, hakan na kara taimakawa kiwon da kuma wadanada suka rungumi shi.
Ana samun nama da madara da fata a jikin Akuya, inda dukkan wadannan abubuwan suke samar da kudi ga wanda yake wannan sana’a.
Haka kuma,kiwon awaki hanya ce ta samar da ayyukan yi, musamman a tsakanin mata na aure da ke kasar nan.
Nau’o’in Akuya:
Akwai nau’o’in awaki da dama, daga cikinsu akwai, wadda ake kira,Boer da Jamnapari da Alpine da Toggenburg da Anglo-Nubian da Saanen da Pygmy da Sahelian da sauransu.
Nau’o’in Akuya wacce Da Aka Fi Kiwo A Nijeriya:
Ana son wanda zai fara kiwon awaki ya tabbatar da ya tantance nau’in Akuya da yake son kiwatawa, musamman don ya samu Nama da Madara masu yawa.
A Nijeriya, akasari an fi kiwata nau’ukan Akuya da ake kira da Gajeru da kuma Matsakaita.
Idan kana son ka zama mai dogora da kai, za ka iya rungumar kiwon awaki kuma za ka samu dimbin kudi daga kiwon, inda ya kuma zama wajibi, ka samu horon da ya dace kafin ka fara wannan kiwo.
Matakai:
Ya zama wajibi ga wanda zai fara yin kiwon awaki, ya tabbatar da ya samu wajen da ya dace, tare da samar da kayan yin kiwon, haka ana son inda za ka yi kiwon, ya kasance a kusa da gari.
Har ila yau, ana son gurin ya kasance ana iya samun Ciyawa don ciyar da Akuyoyin.
Ana Samun Nama Da Madara Daga Awaki:
Ana samun Nama daga Akuya, inda kuma a Nijeriya ake da karin bukatar kiwonta.
Har ila yau, ana samar da madara daga jikin akuya, haka ana yin hada-hadar kasuwancin fatunta.
Idan har za ka fara yin kiwon Akuya a kasar nan, ana bukatar ka dubi kasuwannin cikin gida, musaman kan bukatar da ake da ita ta akuya.
Ciyar Da Ita:
Ana son mai kiwon akuya ya kasance ya tanadar mata da abinci, musamman don ya samu nama mai yawa da kuma madara.
Akasarin wadanda suka ci nasara a kiwon akuya don hada-hadar kasuwancinta,suna ciyar da ita da abincin da ke dauke da sanadarin Furotin.
Bugu da kari, ana son kuma mai kiwonta ya dinga ciyar da ita da abincin da ke dauke da sanadaran bitamins da minerals da salt da sauransu.
Duba Lafiya:
Yana da kyau, mai kiwon akuya ya tabbatar da yana tuntubar likitocin dabbobi don su dinga duba lafiayarsu, tare da samar musu da magungunan da suka dace, idan sun kamu da wata larura.
Dabarun Kasuwancinta:
Wanda yake kiwon akuya, ana son ya tabbatar da ya samar da dabarun yin hada-hadar kasuwancinta da kuma kai su kasuwannin cikin gida da aka fi bukatarsu.
Ana kara samun bukatar awaki a kasar nan, inda hakan ta sa mutane ke kara azama wajen wannan kiwo.