Allah ya yi wa mataimakin shugaban jam’iyyar LP na shiyyar arewa ta tsakiya, Adi Shirsha Adi, rasuwa yana da shekara 61 a duniya.
Kakakin jam’iyyar LP ta ƙasa, Olufemi Arabambi, yace Marigayi Adi ya rasu ne bayan fama da gajeriyar rashin lafiya ranar Laraba.
Jam’iyyar LP ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan marigayin wanda ya fito daga jihar Benuwai.
Mataimakin shugaban jam’iyyar Labour Party (LP) ta ƙasa na shiyyar arewa ta tsakiya, Kwamaret Adi Shirsha Adi, ya rigamu gidan gaskiya.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Sakataren watsa labarai na jam’iyyar LP ta ƙasa, Olufemi Arabambi, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.
Mataimakin Shugaban Jam’iyya Labour Party Na Kasa Ya Rasu Hoto: vanguardngr Yace Kwamaret Adi ya rasu ne ranar Laraba bayan fama da rashin lafiya ta ɗan lokaci yana da shekaru 61 a duniya.
“Shugaban jam’iyya, Barista Julius Abure, a madadin kwamitin gudanarwa da kwamitin zartaswa na LP ta ƙasa, na mai baƙin cikin sanar da rasuwar mataimakin shugaba (arewa ta tsakiya), Adi Shirsha Adi.”
“Ya mutu ne ranar Laraba (9 ga watan Nuwamba, 2022) bayan fama da rashin lafiya ta ɗan lokaci.”
Mun kaɗu da jin labarin – LP Mista Arabambi ya bayyana rasuwar kwamaret Adi a matsayin labarin kaɗuwa, inda yace za’a yi kewar gudummuwarsa wurin kafa gwamnatin da al’umma ke fata.
“Jam’iyya ta shiga jimamin rasuwar Adi Shirsha Adi saboda mutum ne mai sadaukarwa, wanda ya ba da gudummuwa wajen gina LP a shiyyarsa kana ta roki iyalansa su jure wannan rashi.”
“Wannan ba irin labarin da muke fatan yaɗa wa bane, amma a matsayin masu Imani, ba zamu ce meyasa Allah ya ɗauke shi ba, ya fi mu sanin daidai. Bamu da zaɓi sai dai mu gode wa Allah.”
LP ta roki iyalan mamacin su yi koyi da kyawawan halayen mahaifinsu.
Marigayi Adi ya fito ne daga karamar hukumar Konshisha, jihar Benuwai.
Source:legithausang