Wasu mata da miji a jihar Ogun sun shiga hannu bisa zargin suna sana’ar safarar mutane zuwa kasashen waje.
An kama su ne jim kadan bayan da suka sace wata yarinya mai shekaru 16 suka yi kokarin tura ta kasar Burkina Faso.
Ya zuwa yanzu dai ‘yan sanda na ci gaba da bincike don gano tushen lamarin da kuma daukar mataki na gaba.
Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kwamushe wasu mata da miji Godday da Ebere Samuel bisa zarginsu da aikata laifin safarar mutane.
An kame mata da mijin ne a yankin Ota na jihar bisa zargin sun sace wata yarinya mai shekaru 16 mai suna Maria Adeniji.
Jami’in hulda da jama’a a rundunar ‘yan sandan, Abimbola Oyeyemi ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Abeokuta a ranar Litinin, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A cewar Oyeyemi, an kama ma’auratan ne bayan samun rahoton batan yarinyar daga mahaifinta ga ofishin yanki na ‘yan sanda dake Atan Ota.
Yadda aka gano wadanda suka sace yarinyar Mahaifin yarinyar, Adeniji Okikiolu ya shaidawa ‘yan sanda yadda ya rasa diyarsa tare da zargin ma’auratan.
A cewarsa, diyarsa ta bace ne daga gida a ranar Lahadi 16 ga watan Oktoba, yayin da aka tara masu neman inda ta shiga, sai aka gano an ganta tare da Ebere Samuel a washegarin ranar, Premium Times ta ruwaito.
A cewar ‘yan sanda: “Bayan samun bayanai, an gayyaci Ebere Samuel zuwa caji ofis, amma ta kekashe tace bata ga yarinyar ba a ranar ko washegarin ranar.
“Ganin ba a gamsu da bayaninta ba, sai aka tsare ta a caji ofis na dan wani lokaci. ”
Amma abin ban mamaki, lokacin da aka tuntubi mijinta, sai ya amsa cewa sun dauki Maria da ta bata zuwa wani wuri a Legas domin zarcewa da ita zuwa Burkina Faso domin ta yi aiki a can ga wasu abokansu.
“Binciken da aka yi an gano cewa, ma’auratan sun jima suna sana’ar fasarar mutane kuma abokan harkallarsu na can a kasar Burkina Faso.”
Hakazalika, ya bayyana cewa, tuni kwamishinan ‘yan sandan jihar, Lanre Bankole ya umarci a mika batun ga sashen da ya dace domin ci gaba da bincike.
Fasinjoji 13 Sun Kone Kurmus a Wani Hadarin Mota da Ya Rutsa da Su a Enugu.
A wani labarin, akalla fasinjoji 13 ne suka kone kurmus a wani hadarin motan da ya faru a kusa da Four-Corners Enugu da misalin karfe 9 na daren jiya Lahadi, inji rahoton Vanguard.
An ruwaito cewa, motar mai daukar mutane 14 ta taso ne daga jihar Imo a Kudanci inda ta nufi jihar Adamawa a Arewacin Najeriya.
Rahotanni sun bayyana cewa, motar ta shigewa wata babban tirela ne kafin daga bisani ta kama da wuta.
Source:legithausang