Mata 23 Sun Nutse A Cikin Ruwan Maliya A Kasar Sudan.
Kamfanin dillancin labarun Sudan SUNA ya nakalto cewa wani kwale-kwale da yake dauke da mutane 29 ya nutse a cikin ruwan “Blue Nile” a gundumar Sinnar, inda mata 23 da suke cikinsa su ka nitse a ruwa.
Matukin kwale-kwalen da kuma wasu mata biyar sun tsira daga mutuwa a yayin da abin hawan nasu ya yi kulikulin kubura.
Matan da su ka rasa rayukan nasu, leburori ne da suke aikatau a gonakin da suke yankin Souki, kuma suna komawa gida ne a lokacin da hatsarin ya faru.
Tekun na “ Blue-Nile” dai yana da muhimmanci ta bangaren kasuwanci, inda yake isa birnin Khartum sannan kma yake hadewa da tekun maliya.
READ MORE : An Kashe Mutane Da Dama A Wani Hari A Gabashin Kasar Congo.
A shekarar 2018 ma an sami wani hatsari irin wannan da dalibai 22 su ka nitse a cikin jirgin ruwa.