Dubban mutane masu zanga zanga sun tare babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna inda suke zanga-zangar neman gwamnati ta dauki matakan kawo karshen kashe mutane gami da yin garkuwa da su domin karbar kudin fansa da ‘yan bindiga ke yi.
Majiyarmu ta ruwaito cewar tun da misalin karfe 7 na safiyar yau Asabar daruruwan mutane masu zanga zangar suka yi dandanzon rufe babbar hanyar, matakin da ya rutsa da matafiya da dama da suka makale.
Rahotanni sun ce jami’an tsaro na kokarin lallaba masu zanga-zangar domin bude hanyar da suka datse.
Bayanai sun ce zanga-zangar ta biyo bayan karuwar hare-haren ‘yan bindigar akan hanyar ta Abuja zuwa Kaduna da kuma wasu yankunan da ke yankin, inda a baya bayan nan, wasu gungun ‘yan bindiga ska kashe wata karamar yarinya da shekarunta basu wuce 14 ba.
Lamarin dai ya auku ne Unguwar Magaji dake karamar Chikun inda maharan suka sace iyalan Mai Unguwa ko Dagacin garin tare da wani adadi na mazauna yankin.
A wani labarin mai kama da wannan rahotanni daga arewacin Najeriya, sun ce masu yin garkuwa da mutane sun sake tare hanyar Abuja zuwa Kaduna a yammacin jiya Laraba da misalin karfe 3.
Tashin hankalin da ya auku a gaf da kauyen Akilibu ya tilastawa matafiya dakatawa a gefen hanya cikin jiran samun taimakon jami’an tsaro.
Rahotannin sun ce jama’a na cikin zulumin ne, sai aka yi sa’a jerin gwanon motocin Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i suka tunkaro kan hanyar da nufin isa Abuja.
Ba tare da bata lokaci ba, jami’an tsaro madaka kare, dake tare da Gwamnan suka fatattaki ‘yan bindigar, wadanda suka tsere cikin daji.
Karo na uku kenan da masu satar mutane ke cin Karensu ba babbaka a kan hanyar ta Abuja zuwa Kaduna, inda a ranar Litinin suka sace mutane akalla 30, koda yake jami’an yan sabda sun musanta rahoton.
Kwana guda kuma bayan faruwar tashin hankalin, masu satar mutanen suka sake yin awon gaba da wasu matafiya kimanin takwas a dai kan hanyar ta Kaduna zuwa Abuja kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Mutane da dama, na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan matsalar satar mutane da yi garkuwa da su, da ke dada girmama a sassan Najeriya, musamman arewacin Najeriya, inda suka bukaci gwamnati ta ayyana dokar ta baci kan matsalar.