Masu Shigar Da Kara A Burkina Faso Sun Bukaci A Daure Tsohon Shugaban Kasar Saboda Kisan Sankara.
Rahotani daga Burkina Faso sun bayyana cewa Sojoji masu shigar da kasar sun bukaci kotu ta daure tsohon shugaban kasar Blaise Compaore na tsawon shekaru 30 a gidan yari saboda laifin kashe wanda ya gada kuma tsohon shugaban mulkin soji na kasar Thomas sankara a shekara ta 1987.
An fara gudanar da shari’ar ce kan zargin kisan ne bayan da gwamnatin faransa ta amince za ta bada rahoton sojoji dake bayani kan yanayin yadda aka yi kisan,
Haka zalika sun bukaci a daure Hyacinth kofando a gidan yari na tsawon shekaru 30 wanda ake zargi da jagorantar zarata sojojin waken yin kisan gilla ga tsohon dan gwagwarmaya Thomas sankara da mukarrabansa guda 12,
Har ila yau sun bukaci yanke hukumcin zama gidan yari na shekaru 20 ga daure Gilbert Diendere babban wanda ake tuhuma a gaban kotu kuam daya daga cikin kwamandojin soji a lokacin juyin mulkin na 1987 , wanda tuni wata kotu ta yanke masa hukumcin zama gidan yari na shekaru 20 kan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a shekara ta 2015
Yanzu haka dai an dage ci gaba da shari’ar har zuwa watan mayun mai kamawa.