Masu iƙirarin jihadi sun yi garkuwa da shafukan intanet na Mozambique.
Fiye da shafukan intanet 30 a Mozambique – ciki har da na ma’aikatar tsaro – suka durƙushe a ranar Litinin bayan harin da masu kutse suka kai.
“Hacked by Yemeni hackers” shi ne sakon da ake ganin a shafukan na intanet, tare da hoton wani mutum sanye da mayafi kuma yana harba bindiga.
Hukumomin Mozambique sun tabbatar da harin na intanet tare da cewa sun shawo kan matsalar.
Daga cikin wadanda harin ya rutsa da su sun hada da shafukan kula da bala’o’i na kasa da masu kula da tituna da hukumomin ruwa, da ma’aikatar tsaro da cibiyar kula da sufurin kasa.
Hukumomin sun ce babu wata asarar bayanai ko fallasar bayanan sirrin ƴan kasar da aka samu – yayin da wannan shi ne hari na farko mafi girma da aka taba kai wa kasar.
Masharhanta sun yi kira ga gwamnati da ta ƙarfafa matakan tsaro na intanet saboda fargabar cewa mayaka masu ikirarin jihadi ne suka kai harin.