Wasu masu garkuwa da mutane domin binyan Kudin fansa, sun sako ‘yar fasto Daniel Umaru, mai shekaru 13 biyo bayan biyan kudin fansa a garin Kwarhi cikin karamar hukumar Hong a Jihar Adamawa.
Yarinyar da masu garkuwa da mutanen suka sako tana cikin mawuyacin hali, sai dai kuma ba a bayyana yawan adadin kudaden da aka biya kafin ceto rayuwarta.
Rahotanni sun tabbatar da cewa a ranar Asabar ce, aka gudanar da zana’idar ‘yan’uwan yarinyar biyu da masu garkuwa da mutanen suka kashe lokacin da suka je sace yarinyar.
Dama dai a ranar 7 ga watan Yulin 2022, wasu mutane suka shiga gidan Fasto Daniel Umaru, suna ta harbe-harben bindigogi, inda nan take suka kashe ‘ya’yansa biyu tare da yin garkuwa da ‘yarsa mai shekaru 13, yanzu haka dai Faston na ci gaba da karban magani a asibiti.
Majiya daga iyalan yarinyar sun rabbatar da cewa mutanen d suka yi garkuwa da yarinyar sun sako ta biyo bayan biyan makudan kudaden fansa, sai dai majiyar ba ta bayyana yawan kudaden ba.
A wani labarin na daban a wata sanarwa da babban sakataren JNI, Dakta Khalid Abubakar Aliyu, ya fitar ranar Alhamis a Kaduna, Amirul Muminin ya kuma bukaci alhazan Nijeriya da su yi wa Nijeriya da shugabanninta addu’a na musamman, yayin da suke tsaye a kan dutsen Arafat.
Sanarwar ta kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su nemi taimakon Allah domin samun kwanciyar hankali, tsaro da zaman lafiya da ci gaban Nijeriya a daidai lokacin da babban zaben shekarar 2023 ke gabatowa.
JNI, ta sake nanata bukatar yin addu’o’i sosai domin samun sauye-sauyen siyasa cikin lumana, da kuma kawo karshen kalubalen zamantakewa da tattalin arziki iri-iri a kasar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa:
“Idan aka yi la’akari da cewa al’amura guda biyu suna haduwa a ranar Juma’a, wato gobe akwai bukatar tunatar da musulmi da su yi azumin ranar 9 ga watan Zul-Hijja (Arafat), kamar yadda Annabi (SAW) ya koyar da shi. kasancewarta rana ta musamman ta Juma’a kuma ita ce mafificiyar ranar mako, a cikinta ake yin Sallar Juma’a da amsa addu’o’i a cikin sa’a ta musamman da Arafat – mafi kyawun ranar shekara a cikinta. Allah mai rahama yana gafartawa bayinsa kuma yana amsa dukkan addu’o’in ranar Arafat.
“Don haka Mai Martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, CFR, mni, ya bukaci al’umar Musulmin Nijeriya da su azumci ranar, kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya koyar kuma a yi addu’a neman Allah Madaukakin Sarki da ya shiga lamuranmu.
Source:hausalegitng