Sakamakon yadd ayyukan masu aikin gayya da taimakon kai da kai suke dab da bacewa a tsakanin al’umma, wasu masu fashin baki sun kawo shawarar yadda za a farfado da lamarin samun saukin rayuwa musamman a wannan lokaci da ake ganin rayuwa ta yi kunci.
Masu fashin bakin, Alhaji Aliyu Musa Turaki (Tafidan Gurku) wanda har ila yau shi ne shugaban kungiyar ci gaban al’umma ta Mararrabar Gurku da kuma Sabo Imam Gashuwa, sun bayar da shawarar ce a Shirin Barka Da Hantsi Nijeriya na Kamfanin LEADERSHIP da ake gabatarwa daga ranakun Litinin zuwa Jumma’a da misalign karfe 9 na safe, kai-tsaye a shafin YouTube da Facebook.
A bangarensa, Alhaji Aliyu Musa Turaki ya yi kira ga mutane masu neman cigaban al’umma su sake tunani wajen taimakawa kansu da kansu, sannan kuma su hada kai domin sai da shi ne za su samu damar taimakawa kansu musamman ma tsaftace muhalli da ke da matukar muhimmanci. Yana mai cewa, “Domin da talakawan wannan zamani za su gudanar da aikin gayya kamar yadda yake guda a shekarun baya, da za a samu ci gaba.”
Ya kuma yi kira ga shugabanni su yi amfani da damar da Allah ya ba su tare da tunawa da hakkin da ya rataya a kansu inda ya ce matukar shugabanni ba su taimaka ba, farfadi da ayyukan gayya zai yi wahala.
Ya yi nuni da irin halin da harkar ilmi take a Arewacin Nijeriya. Ya kara da cewa “idan har mutane suka fara taimakawa kansu kamar dai yadda ake a shekarun da suka gabata, zai sa gwamnati ta shigo cikin al’amuransu gadan- gadan.”
Shi ma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Sabo Imam, cewa ya yi akwai babban kalubale kan shugabanni, “saboda bai dace a ce su wadanda Allah ya dora wa alhakin al’amuran talakawa su tsaya daga su sai ‘ya’yansu ba.”
Ya yi kira ga mutane su rika kulawa da gyara abubuwan da gwamnati take yi saboda jin dadinsu, “alal misali su rika zuba shara wurin da aka tanadar domin abin daga karshe na iya taimakawa wajen samar da ambaliyar ruwa idan aka ci gaba da yin hakan. Sannan ga matsalar yadda cutar kwalara take ci gaba da kashe mutane, kuma kowa ya sani rashin tsaftar muhalli yana taimakawa wajen yaduwar cutar.” In ji shi.