Wasu mutane da ake zargin masu fasa-kwauri ne sun hallaka wani jami’in Hukumar Hana Fasa-Kwauri ta Kasa (Kwastam) ranar Asabar a yankin Owode da ke Karamar Hukumar Yewa ta Kudu a Jihar Ogun.
Jami’in dai mai mukamin Custom Assistant 1 shi ne direban da ke aiki da Sashen Ayyuka na Musamman na hukumar.
Kakakin shiyya ta daya na hukumar da ke Legas, Theophilus Duniya ne ya tabbatar da kai harin ga wakilinmu ranar Lahadi, ko da dai bai bayyana sunan jami’in ba.
Duniya ya ce tun da farko dai hukumar ta kama motocin masu fasa kwaurin ne ne inda a yayin yunkurin kai su zuwa Legas daya daga cikinsu ta lalace a kan hanya kuma aka tsaya gyara ta.
A cewarsa, “Ana cikin gyaran ne sai masu fasa-kwaurin suka yo tururuwa dauke da muggan makamai da kayan asiri har suka sami nasarar kashe jami’in namu.
“Yanzu haka mun kai gawarsa zuwa sashen adana gawarwaki a asibiti,” inji shi.
Ya ce tuni mai rikon mukamin babban kwaturolan hukumar na shiyya ta daya ya bayar da umarnin a gaggauta fara binciken musabbabin kisan.
Kakakin ya kuma ce kwanturolan ya yi Allah-wadai da kisan inda ya ce hakan ba zai sa su yi kasa a gwiwa ba kan yakin da hukumar ke yi da masu fasa-kwauri.
A wani labarin na daban ranar Talata 11 ga Satumban 2001, ne wasu masu alaka da kungiyar al- Ka’ida su 19 suka kwace jiragen sama guda 4 tare da kai hare-haren kunar bakin wake a Amurka kan tagwayen gine gine na Cibiyar kasuwanci ta Duniya da ke birnin New York, da ma’aikatar tsaro ta Pentagon da ke Washington, yayin na fado, a jihar Pennsylvania.
Kusan mutane 3,000 suka mutu yayin harin wanda ya kasance mani muni a tarihin Amurka.
Shugaban Amurka Joe Biden, sabanin shugabanin da suka gabace shi, ya fitar da wani faifan bidiyo maimakon yin jawabi yayin bikin zagayowar ranar inda ya bukaci Amurkawa dasu hada kansu, wanda shi ne karfin kasar inji shi.
Kafin hakan dai, Mista Biden ya ba da umarnin sakin wasu bayanan sirri dangane da binciken gwamnati kan harin na ranar 11 ga watan satumban 2001.