Babu shakka Gwamna Aminu Bello Masari da mukarraban Gwamnatinsa da ma al’umar Jihar Katsina sun nuna hakuri, juriya tare da dukufa ga rokon Allah Ya kawo mafita a cikin lamarin tsaro.
Gwamna Aminu Masari ka zubar da hawayen ka ba adadi a boye da a bainar jama’a saboda ganin aikin rashin Imani da jahilci da rashin tausayi da wasu ‘yantsiraru suka aikata ga jama’arka wadanda ba su ji ba, ba su gani ba. Hakika, kai da wasu Jami’an Gwamnatinka kun gamu da jarabawa, da cin kashi iri-iri, a kokarinku na fahimtar da mutane illar ta’addanci da kuma muhimmancin zaman lafiya.
A dukkan wuraren da aka ziyarta a yayin zagaye na biyu na yunkunrin kashe fitinar ta hanyar lalama, Maigirma Gwamna Masari kan gargade su a kan cewa ” kada fa ku sake mu janye hannunmu, mu bar ku da Sojoji, domin shi Soja babu abin da ya sani sai yaki.” Yakan ma kara da cewa ” Mu, zubar da jinin ne ba mu so, kuma ba mu son a lalata kasar. Amma ku sani, in yau kuka kashe Soja goma, gobe Gwamnatin Tarayya za ta kawo dari. Idan kuka kashe dari kuma, za ta turo Soja dubu.”
To, tunda duk wannan bayanin tare da lallashi da aka yi ta faman yi, ya bi ta bayan kunnensu, wa kuma yake da bakin magana yanzu?
Da dama, na ganin cewa; Allah ne Ya karbi addu’o’in da ake yi, tare da amsa kiraye-kirayen da Gwamnatin Jihar Katsina karkashin mai girma gwamna Masari ta dade tana yi ga makwaftanmu na su dauki mataki na bai daya. Su kuma Rundunonin Jami’an Tsaro su yi aiki tare kuma, su kamo bai daya daga kowace jiha, su kutsa kai, su iske mutanen can har maboyarsu a yi ta, ta kare.
Daga labarun da muke ji “Wallahi”, ku sani, Gwamnatocinmu da Jami’an Tsaro, ‘yan Nijeriya na jinjina muku. Muna da kyakkyawar fatar cewa ba za ku tsaya ba har sai kun gama aikin nan baki dayansa.
Babu mai wani shakku game da kwarewarku ko jaruntakarku ko sadaukarwa da naci wajen aiwatar da aikin da dokar kasa ta dora muku. Tarihi ba zai manta da irin muhimmiyar rawar da Sojan Nijeriya suka taka ba wajen kai dauki ga kasashen Turai a lokacin yakin duniya na biyu; 1944.
A nan kusa ma cikin Nahiyar Afirika, muna sane da irin gagarumar gudummuwar da ku Sojoji da abokan aikinku wato ‘Yansandan Nijeriya kuka bada wajen kawar da zalunci da tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a kasashe irin su, Sudan, Somaliya, Laberiya, Saliyo da sauransu wadanda ba don ku ba, watakila da tuni sun zama kufai.
Saboda haka, mafi rinjayen ‘yan Nijeriya, musamman dai mu a nan Jihar Katsina mun yi imani cewa idan dai Gwamnatin Tarayya ta wadata ku da kayan aiki na kirki, kuma Kwamandojinku suka samu cikakken hadin kai da sakin mara daga Shugabanninsu, kana aka fitar da son zuciya da zari ko siyasa, aka yi aiki tare ya ka junanku, to tabbas!
A cikin ‘yan makonni za ku lakume wadan nan ‘yan bankaurar.Wanda duk ya taba kashe rai ko ya ci mutunci wata mace ko ya gallazawa jama’a a cikin su kada Allah Ya ba shi hanyar tsira daga aikin da kuke yi a halin yanzu.
Bari in taba wani kirari da na kan ji wani yayana tsohon soja na yi tun ina karami. Allah ya jikan Malam Tukur, idan yana ba mu labarin yakin Ujukku a wani zubin idan ya tuno da wani abin sai ya zabura ya mike tsaye, ya buga kafa kanayakame kyam! Kana ya fadi da karfi cewa: “Haba Soja – Haba Soja, Maza kuke ba Mata ba. Soja birgimar hankaka, kowa ya ga bakinku, zai ga farinku. Soja na Gwamna ga rawa ga yaki. Bariki ba gayya ba, kowa ya bi Allah ya shiga” Muna rokon Allah Ya yi maku jagora, Ya ba ku nasara. Muna godiya. A fito lafiya.
A naku bangaren ya Maigirma Gwamna Masari , muna rokon Allah Ya kara muku hakuri da juriya a kan halayen wasunmu wadanda ba za su taba yaba wa kokarin da kuke yi ba. Ku dai ku himmatu wajen yin abin da ya dace kai da mukarrabanka. Allah Ya iya muku a inda ba ku iyawa. Ya kuma tabbatar mana da dawamammen zaman lafiya da ci gaba a Jihar Katsina da jihohi makwabtanmu da kasa baki daya.
Muna rokon Allah Ya gafarta wa dukkan wadanda suka rasa rayukansu a hannun ‘yan ta’addar nan, Allah ka kubutar da wadanda duk suke tsare a hannunsu, Ka kame hannayensu daga cin mutunci ko cutar da su ta kowace hanya, wadanda suka rasa dukiyarsu ko wani nasu kuma, Ya Allah Ka ba su hakuri, Ka kuma mayar musu da mafificin alheinka.
Ya Allah Ka taimaki Shugabanninmu da Jami’an Tsaronmu da sauran wadanda duk suke kokari wajen magance matsalar tsaron nan. Ya Allah Ka kuma tona asirin wanda duk yake da hannu wajen taimakawa ‘yan ta’addar nan ta kowace hanya. Masu shiryuwa a cikinsu, Ka shiryar da su, wadanda ba su shiryuwa, Allah Ka san su, Ka hada su a gama da su, bayinka mu huta.
Da fatan mu kuma jama’a za mu hankalta, mu nace da yin addu’oi, tare da nuna kishi ta hanyar bada cikakken goyon baya da hadin kai musamman wajen tabbatar da ganin mun taka burki ga duk wanda muka ga zai karya duk wata dokar da Gwamnati ta bullo da ita don yaki da matsalar tsaron nan ta hanyar da ta dace.
Su kuwa wadancan mutanen ga su, ga jami’an tsaron nan.
‘Yan magana kan ce: Duk wanda bai ji bari ba, ya ji hoho. Kuma ita “bari” ba….