Yayin da ake tsaka da rikicin masarautar Kano, Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ya daga tutar mulki a karamar fadar da ke Nassarawa.
Wannan yana nuna iko da Sarkin yake da shi a yanzu.
A bisa al’ada, tutar na zama ne a matsayin alamar iko, kuma daga ta na alamta cewa sarki yana cikin fada.
Wannan kuwa na zuwa ne duk da umarnin gwamnatin Kano ga Sarki Aminu ya fice daga fadar a yayin da ake ci gaba da dambarwar sarautar Kano.
Akan daga tutar ce da misalin karfe 6 na safe a kuma sauke ta 6 na yamma ko idan sarki ya yi bulaguron aiki.
Kano ta shiga rikicin masarauta tun bayan da gwamnatin jihar ta rushe masarautun Bichi, Karaye, Rano da Gaya wanda tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro.
Rikicin na ci gaba da haifar da rudani yayin da Aminu Ado Bayero da Sarkin Kano na 14, Muhammdu Sanusi II kowa ke ci gaba da ikirarin shi ne Sarkin Kano.
A wani labarin na daban bayan kammala wa’adin Farfesa AbdulRasheed Na’Allah, a matsayin Shugaban Jami’ar Abuja (UniAbuja), na 6 a ranar 30 ga Yunin 2024, hukumar gudanarwar Jami’ar ta zabi Farfesa Aisha Sani Maikudi a matsayin mukaddashiyar shugabar jam’iar har zuwa lokacin da za a nada sabon shugaban.
Ta kasance Farfesa a fannin shari’a ta kasa da kasa kuma mataimakiyar shugaban jami’a a fannin ilimi a yanzu.
Ta yi karatu a Jami’a a Ingila, inda ta samu digirinta na farko da na biyu a kan shari’a sannan ta halarci makarantar aikin lauya ta Nijeriya, da ke Abuja, kana ta wuce Jami’ar Abuja don neman digirin digirgir.
Maikudi ta fara aiki da Jami’ar Abuja, a matsayin malama kuma ta zama mace ta farko karamar shugabar Sashen Koyarwar Shari’a a 2014.
DUBA NAN: Zafi Yayi Sanadin Mutuwar Fiye Da 900 A Hajjin Bana
Har wa yau ta kasance mace ta farko da ta rike mataimakiyar shugaban tsangayar shari’a a 2018, da kuma mukamin babbar daraktan Jami’ar Abuja.